Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 41:22-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Ku zo nan ku faɗi abin da zai faru nan gaba,Ku bayyana wa ɗakin shari'a abubuwan da suka riga sun faru,Ku faɗa mana yadda zai zama duka,Domin lokacin da ya faru mu mu sani.

23. Ku faɗa mana abin da gaba ta ƙunsa.Sa'an nan za mu sani, ku alloli ne!Ku aikata wani abu mai kyau, ko ku kawo wani bala'i,Ku cika mu da jin tsoro da fargaba!

24. Ku da dukan abin da kuke yi ba kome ba ne,Waɗanda suke yi muku sujada kuwa,Abin ƙyama ne su!

25. “Na zaɓi mutum wanda yake zaune a gabas,Zan kawo shi don ya kawo hari daga arewa.Zai tattake masu mulki su zama kamar lāka,Kamar yadda magini yake tattake yumɓu.

26. Wane ne a cikinku ya faɗa mana tun da wuri,Ko ya yi annabci, cewa wannan zai faru,Har da za mu ce kun yi daidai?Ba ko ɗayanku da ya ce tak a kan wannan,Ba kuwa wanda ya ji kuna faɗar wani abu!

27. Ni Ubangiji, ni ne na farko da na faɗa wa Sihiyona albishir,Na aiki manzo zuwa Urushalima don ya ce,‘Jama'arki suna zuwa! Suna zuwa gida.’

28. Sa'ad da na duba alloli,Ba wanda yake da abin da zai faɗa,Ko ɗaya, ba wanda ya iya amsa tambayar da na yi.

29. Dukan waɗannan alloli ba su da amfani,Ba su iya kome ba, ko kaɗan,Gumakansu ba su da ƙarfi, ba su kuma da iko!”

Karanta cikakken babi Ish 41