Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 41:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Allah ya ce,“Ku yi shiru ku kasa kunne gare ni, ku manisantan ƙasashe!Ku yi shiri ku gabatar da ƙararku a ɗakin shari'a.Za ku sami zarafi ku yi magana.Bari mu taru mu ga wanda yake da gaskiya.

2. “Wane ne wannan da ya kawo mai yin nasara daga gabas,Ya kuma sa ya ci nasara a dukan inda ya tafi?Wa ya ba shi nasara a kan sarakuna da al'ummai?Takobinsa ya sassare su sun zama kamar ƙura!Kibansa sun warwatsar da su kamar ƙaiƙayi a gaban iska!

3. Yana biye da kora, yana kuma tafiya lafiya,Da sauri ƙwarai, da ƙyar yake taɓa ƙasa!

4. Wane ne ya sa wannan ya faru?Wane ne ya ƙudurta labarun tarihi?Ni Ubangiji, ina can tun da farko,Ni kuma Ubangiji Allah,Zan kasance a can har ƙarshe.

5. “Mutanen manisantan ƙasashe suka ga abin da na yi,Suka tsorata, suka yi rawar jiki saboda tsoro.Saboda haka duka suka tattaru wuri guda.

6. Masu aikin hannu suka taimaka suka ƙarfafa juna.

7. Masassaƙi yakan ce wa maƙerin zinariya, ‘A gaishe ka!’Wanda yake gyara gumaka ya yi sumulYana ƙarfafa wanda yake harhaɗa su.Wani yakan ce, ‘Haɗin ya yi kyau,’Sukan kuma manne gumakan da ƙusoshi.

8. “Amma kai, Isra'ila bawana,Kai ne jama'ar da na zaɓa,Zuriyar Ibrahim, abokina,

9. Na kawo ka daga maƙurar duniya,Na kira ka daga kusurwoyi mafi nisa.Na ce maka, ‘Kai ne bawana.’Ban ƙi ka ba, amma maimakon haka na zaɓe ka.

10. Kada ka ji tsoro, ina tare da kai,Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka.Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka,Zan kiyaye ka, in cece ka.

11. “Su waɗanda suke fushi da ku, ku jama'ata,Za a ƙasƙantar da su su ji kunya.Waɗanda suke faɗa da ku kuwa za su mutu.

12. Za ku neme su, amma ba za ku same su ba,Wato waɗanda suke gāba da ku.Waɗanda suka kama yaƙi da ku,Za su shuɗe daga duniya.

13. Ni ne Ubangiji Allahnku,Na ƙarfafa ku, na kuwa faɗa muku,‘Kada ku ji tsoro, ni zan taimake ku.’ ”

14. Ubangiji ya ce,“Isra'ila, ku kima ne marasa ƙarfi kuma,Kada ku ji tsoro, zan taimake ku.Ni Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ni ne mai fansarku.

15. Zan sa ku zama kamar abin sussuka,Wanda yake sabo, mai kaushi, mai tsini.Za ku sussuke duwatsu ku lalatar da su,Za a marmashe tuddai kamar ƙura.

Karanta cikakken babi Ish 41