Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 40:23-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Yakan kawo masu mulki masu iko ƙwarai,Ya kuwa mai da su ba kome ba ne,

24. Suna kama da ƙaramin dasheWanda bai daɗe ba,Bai yi ko saiwar kirki ba.Sa'ad da Ubangiji ya aiko da iska,Sai su bushe, iskar ta hure su kamar ƙaiƙayi.

25. Da wane ne za a kwatanta Allah Mai Tsarki?Ko akwai wani mai kama da shi?

26. Ka dubi sararin sama a bisa!Wane ne ya halicci taurarin da kake gani?Shi wanda yake musu jagora kamar sojoji,Ya sani ko su guda nawa ne,Yana kiran dukansu, ko wanne da sunansa!Ikonsa da girma yake,Ba a taɓa rasa ko ɗayansu ba!

27. Isra'ila, me ya sa kake gunaguni,Cewa Ubangiji bai san wahalarka ba,Ko ya kula ya daidaita abubuwa dominka?

28. Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba?Ubangiji Madawwamin Allah ne?Ya halicci dukkan duniya.Bai taɓa jin gajiya ko kasala ba.Ba wanda ya taɓa fahimtar tunaninsa.

29. Yakan ƙarfafa masu kasala da masu jin gajiya.

Karanta cikakken babi Ish 40