Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 40:11-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Zai lura da garkensa kamar yadda makiyayi suke yi,Zai tattara 'yan raguna wuri ɗaya,Zai ɗauke su ya rungume su,A hankali zai bi da iyayensu.

12. Akwai wanda zai iya auna teku da tafin hannu,Ko sararin sama da tafin hannunsa?Akwai wanda zai iya tallabe turɓayar duniya a cikin finjali,Ko ya iya auna duwatsu da tuddai a ma'auni?

13. Akwai wanda zai iya umartar Ubangiji ya yi abu?Wa zai iya koya wa Ubangiji, ko ya yi masa shawara?

14. Da wa Allah yake yin shawaraDomin ya sani, ya kuma fahimta,Ya kuma koyi yadda za a yi abubuwa?

15. Al'ummai ba kome ba ne a wurin Ubangiji,Ba su fi ɗigon ruwa ba,Manisantan tsibirai ba su fi ƙura nauyi ba.

16. Dukan dabbobin da yake a jejin LebanonBa su isa hadaya guda ga Allahnmu ba,Itatuwan jejin kuma ba su isa a hura wuta da su ba.

17. Al'ummai ba kome ba ne ko kaɗan a gare shi.

18. Da wa za a iya kwatanta Allah?Wa zai iya faɗar yadda yake?

19. Shi ba kamar gunki yake ba, wanda mutane suka yi,Maƙera kuma suka dalaye da zinariya,Suka sa shi cikin abin da suka yi da azurfa.

20. Mutum wanda bai isa samun azurfa ko zinariya ba,Yakan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba.Yana neman gwanin sassaƙaDomin ya yi masa siffa wadda ba za ta fāɗi ba.

21. Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba?Ashe, ba a faɗa maka ba tuntuni?Ashe, ba ka ji yadda aka fara duniya ba?

22. Wanda yake zaune a kursiyi ne ya yi ta,Can ƙwanƙolin duniya, gaba kuma da sararin sama,Yana ganin mutane a ƙarƙas kamar 'yan ƙananan ƙwari.Ya miƙa sararin sama kamar labule,Kamar kuma alfarwa domin mutane su zauna ciki.

23. Yakan kawo masu mulki masu iko ƙwarai,Ya kuwa mai da su ba kome ba ne,

24. Suna kama da ƙaramin dasheWanda bai daɗe ba,Bai yi ko saiwar kirki ba.Sa'ad da Ubangiji ya aiko da iska,Sai su bushe, iskar ta hure su kamar ƙaiƙayi.

Karanta cikakken babi Ish 40