Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 36:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta goma sha huɗu da Hezekiya yake sarautar Yahuza, sai Sennakerib Sarkin Assuriya ya tasar wa birane masu kagara na Yahuza, ya kame su.

2. Sa'an nan ya umarci babban shugaban yaƙinsa ya tashi daga Lakish ya tafi Urushalima tare da babbar rundunar mayaƙa don su sa sarki Hezekiya ya ba da kai. Sai shugaban ya mamaye hanya inda masu wankin tufafi suke aiki, a daidai magudanar da yake kawo ruwa daga kududdufin da yake daga can bisa.

3. Mutanen Yahuza su uku suka fito don su tarye shi, shugaba mai lura da fāda, wato Eliyakim ɗan Hilkiya, da marubucin ɗakin shari'a, wato Shebna, da shugaban da yake kula da tarihin da aka rubuta, wato Yowa ɗan Asaf.

4. Sai shugaban Assuriyawa ya faɗa musu, cewa babban sarki yana so ya san ko me ya sa sarki Hezekiya yake dogara ga kansa.

5. Ya ce, “Kana tsammani magana da baki kawai ta isa ta yi aiki da gwanayen sojoji, da kuma masu ƙarfi? Wa kake tsammani zai taimake ka, har da za ka yi mini tawaye?

6. Kana sa zuciya Masar za ta taimake ka, to, wannan ya zama kamar ka ɗauki kyauro ya zama sandan dogarawa, zai karye, ya yi wa hannunka sartse. Haka Sarkin Masar yake ga duk wanda ya dogara gare shi.”

7. Ya ci gaba ya ce, “Ko za ka ce mini kana dogara ga Ubangiji Allahnka? Shi ne wannan da Hezekiya ya lalatar masa da wuraren sujada da bagadai, sa'an nan ya faɗa wa jama'ar Yahuza da na Urushalima su yi sujada ga bagade ɗaya kurum.

8. Zan yi ciniki da kai da sunan babban sarki, wato Sennakerib. Zan ba ka dawakai dubu biyu idan za ka iya samun yawan mutanen da za su hau su!

9. Ba ka yi daidai da ka ƙi ko wani marar maƙami a shugabannin Assuriya ba, duk da haka kana sa rai ga Masarawa su aiko maka da karusai, da mahayan dawakai!

10. Kana tsammani na tasar wa ƙasarka na kuma lalatar da ita ba tare da taimakon Ubangiji ba? Ubangiji da kansa ne ya faɗa mini in tasar wa ƙasarka in lalatar da ita.”

Karanta cikakken babi Ish 36