Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 31:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Waɗanda suka tafi Masar neman taimako, sun shiga uku! Suna dogara ga ƙarfin tulin dawakan Masar na yaƙi, da karusansu, da sojojinsu. Amma ba su dogara ga Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila ba, ba su ko roƙe shi taimako ba.

2. Ya san abin da yake yi! Zai aika da bala'i. Zai ci gaba da niyyarsa ta hukunta wa mugaye duk da masu kiyaye su.

3. Masarawa su ba Allah ba ne, mutane ne kurum! Dawakansu ba su wuce ikon ɗan adam ba! Sa'ad da Ubangiji zai matsa, ƙaƙƙarfar al'umma za ta marmashe, al'ummar da aka yi wa taimako kuma za ta fāɗi. Dukansu za su hallaka.

4. Ubangiji ya ce mini, “Kamar dai makiyaya ba za su iya tsoratar da zakin da ya kashe dabba ba, kome irin tsawa da ihun da suka yi, haka ni ma, ba abin da zai iya hana ni, ni Ubangiji Mai Runduna, in kiyaye Dutsen Sihiyona.

Karanta cikakken babi Ish 31