Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 30:9-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. A kullum suna tayar wa Allah, a kullum ƙarya suke yi, a kullum suna ƙin kasa kunne ga koyarwar Allah.

10. Sukan faɗa wa annabawa su yi shiru. Sukan ce, “Kada ku yi mana magana a kan abin da yake daidai. Ku faɗa mana abin da muke so mu ji ne kawai. Bari mu ci gaba da ruɗewarmu.

11. Tashi daga nan, kada ku toshe mana hanya. Ba ma so mu ji kome game da Allah Mai Tsarki na Isra'ila.”

12. Amma wannan shi ne abin da Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya ce, “Kun yi banza da abin da nake faɗa muku, kuna dogara ga aikin kamakarya da yin zamba.

13. Kun yi laifi. Kuna kamar bango wanda ya tsage daga bisa har ƙasa. Za ku fāɗi ba zato ba tsammani.

14. Za a ragargaza ku kamar tukunyar yumɓu, da mummunar ragargazawa har da ba za a sami 'yar katangar da za a ɗauki garwashin wuta ba, ko a ɗebo ruwa daga randa.”

15. Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya ce wa jama'a, “Ku komo gare ni a natse, ku dogara gare ni. Sa'an nan za ku zama ƙarfafa ku zauna lafiya.” Amma ba ku yarda ba!

16. A maimakon haka sai kuka shirya ku tsere wa maƙiyanku a kan dawakai masu gudu. Daidai ne, tilas ku tsere! Tsammani kuke saurin gudun dawakanku ya isa, amma waɗanda za su fafare ku sun fi ku gudu!

17. Dubunku za su gudu da ganin abokin gābanku ɗaya, abokan gāba biyar sun isa su sa dukanku ku gudu. Ba abin da zai ragu daga cikin rundunar sojojinku, sai sandan tutarku kaɗai da take kan tudu.

18. Duk da haka dai, Ubangiji yana jira ya yi muku alheri. A shirye yake ya yi muku jinƙai, domin a kullum yana aikata abin da yake daidai. Ta wurin dogara ga Ubangiji ake samun farin ciki.

19. Ku jama'ar da suke zaune a Urushalima ba za ku ƙara yin kuka ba. Ubangiji mai juyayi ne, sa'ad da kuka yi kuka gare shi neman taimako, zai amsa muku.

20. Ubangiji zai sa ku ku sha wahala, amma shi kansa zai kasance tare da ku, ya koya muku, ba za ku ƙara wahalar nemansa ba.

Karanta cikakken babi Ish 30