Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 3:17-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Amma zan hukunta su, in aske kawunansu, in bar su ƙwal.”

18. Rana tana zuwa sa'ad da Ubangiji zai raba matan Urushalima da dukan abin da suke taƙama da shi, da kayan adon da suke sawa a ƙafafunsu, da kawunansu, da wuyansu,

19. da hannuwansu. Zai raba su da lulluɓinsu,

20. da hulunansu. Zai raba su da layun da suke sa wa damatsansu, da kwankwasonsu,

21. da ƙawanen da suka sa a yatsotsinsu da hancinsu.

22. Ubangiji zai raba su da dukan kyawawan rigunansu na ado, da manyan rigunansu, da mayafansu, da jakunkunansu,

23. da rigunansu na yanga, da ƙyallayensu na lilin, da adikai, da gyale masu tsawo waɗanda suke sawa a kawunansu.

24. Maimakon su riƙa ƙanshin turare, za su yi wari, a maimakon abin ɗamara, za su yi ɗamara da igiyoyi masu kaushi, a maimakon su kasance da kyakkyawan gashi, za su zama masu sanƙo, a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki, kyansu zai zama abin kunya!

25. Jama'ar garin, i, har da ƙarfafan mutane, za a kashe su a yaƙi.

26. Ƙofofin birnin za su yi makoki, su yi kuka.Za a kamanta birnin da matar da take zaune a ƙasa tsirara.

Karanta cikakken babi Ish 3