Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 17:7-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. A wannan rana, mutane za su juyo neman taimako ga Mahaliccinsu, Allah Mai Tsarki na Isra'ila.

8. Ba za su ƙara dogara ga bagaden da suka yi da hannuwansu ba, ko kuwa su dogara ga ayyukan hannuwansu, ko keɓaɓɓun wuraren da suke wa gumaka sujada, ko bagadai don ƙona turare.

9. A wannan rana, za a watse a bar birane masu ƙaƙƙarfar kagara su zama kufai a jeji kuwa kamar rassan da aka watsar a gaban jama'ar Isra'ila.

10. Isra'ila, kin manta da Allah wanda ya kuɓutar da ke, wanda ya kāre ki kamar babban dutse. Kin dasa wa kanki lambuna masu ni'ima don ki yi wa gumaka sujada.

11. Amma ko da za su toho su yi fure a safiyar da kuka dasa su, duk da haka ba za a girbe kome ba. Wahala ce kaɗai da azabar da ba ta warkuwa.

12. Al'ummai masu iko sun hargitse suna ta rugugi kamar rurin teku, kamar karon manyan raƙuman ruwa.

13. Al'ummai sun ci gaba kamar sukuwar raƙuman ruwa, amma Allah ya tsauta musu suka kuwa janye, aka kora su kamar ƙura a gefen dutse, kamar kuma tattaka a cikin guguwa.

14. Da maraice sukan ba da tsoro, amma da safe ba su! Wannan ita ce ƙaddarar duk wanda ya washe ƙasarmu!

Karanta cikakken babi Ish 17