Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 10:7-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Amma Sarkin Assuriya yana da nasa mugayen shirye-shirye da zai yi. Ya yi niyya ya hallaka al'ummai masu yawa.

8. Ya yi kurari, ya ce, “Kowane shugaban mayaƙana sarki ne!

9. Na ci biranen Kalno da na Karkemish. Na ci biranen Hamat da na Arfad. Na kuma ci Samariya da Dimashƙu.

10. Na miƙa hannuna don in hukunta wa waɗannan mulkoki masu bauta wa gumaka, wato gumakan sun yi yawa fiye da na Urushalima, da na Samariya.

11. Na hallaka Samariya da dukan gumakanta, haka ma zan yi wa Urushalima da siffofin da suke yi wa sujada a can.”

12. Ubangiji ya ce, “Sa'ad da na gama abin da nake yi a kan Dutsen Sihiyona da cikin Urushalima, zan hukunta Sarkin Assuriya saboda dukan kurarinsa da girmankansa.”

13. Sarkin Assuriya ya yi kurari ya ce, “Dukan waɗannan ni da kaina na yi su. Ni ƙaƙƙarfa ne, mai hikima, mai wayo. Na kawar da kan iyakokin da suke tsakanin ƙasashen sauran al'umma, na kwashe dukan abin da suka tattara suka adana. Kamar bijimi, haka na tattake mutanen da suke zaune a can.

14. Al'umman duniya kamar sheƙar tsuntsaye suke. Na tattara dukiyarsu, a sawwaƙe kamar yadda ake tattara ƙwai, ba tsuntsun da ya buɗe baki don ya yi mini kuka!”

15. Amma Ubangiji ya ce, “Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma? Ko zarto ya fi wanda yake amfani da shi muhimmanci? Ba kulki yake riƙe da mutum ba, amma mutum yake riƙe da kulki.”

16. Ubangiji Mai Runduna zai aukar da cuta don ya hukunta waɗanda suke ƙosassu yanzu. Za su ji jikinsu na ta ƙuna kamar wuta.

Karanta cikakken babi Ish 10