Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 10:16-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ubangiji Mai Runduna zai aukar da cuta don ya hukunta waɗanda suke ƙosassu yanzu. Za su ji jikinsu na ta ƙuna kamar wuta.

17. Allah da yake hasken Isra'ila, zai zama wuta. Allah, Mai Tsarki na Isra'ila, zai zama harshen wuta, wanda zai ƙone kowane abu rana ɗaya, har da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya.

18. Jeji mai dausayi da ƙasar noma za a lalatar da su ƙaƙaf, kamar yadda ciwon ajali yake hallaka mutum.

19. Sai 'yan itatuwa kaɗan za su ragu, ko ɗan ƙaramin yaro ma zai iya ƙidaya su.

20. Lokaci zai yi sa'ad da jama'ar Isra'ila da suka ragu ba za su ƙara dogara ga al'ummar da ta kusa hallaka su ba. Hakika za su dogara ga Ubangiji Allah, Mai Tsarki na Isra'ila.

21. Kaɗan daga cikin jama'ar Isra'ila za su koma wurin Allahnsu Mai Iko Dukka.

22. Ko da yake yanzu akwai jama'ar Isra'ila da yawa, yawansu kuwa kamar yashin teku, duk da haka, sai kaɗan ne za su komo. An tanada wa jama'a hallaka, sun kuwa cancanci hallakar.

23. Hakika a ƙasar duka, Ubangiji Allah Mai Runduna zai kawo hallaka kamar yadda ya ce zai yi.

24. Ubangiji Mai Runduna ya ce wa jama'arsa da suke Sihiyona, “Kada ku ji tsoron Assuriyawa, ko da yake suna wahalshe ku kamar yadda Masarawa suka yi.

25. Saura kaɗan in gama hukuncin da nake yi muku, sa'an nan in hallaka su.

26. Ni, Ubangiji Mai Runduna, zan bulale su da bulalata, kamar yadda na bugi mutanen Madayana a dutsen Oreb. Zan sa Assuriyawa su sha wahala kamar yadda Masarawa suka sha.

27. A lokacin nan zan 'yantar da ku daga mulkin Assuriya, karkiyarsu ba za ta ƙara zama kaya mai nauyi a wuyanku ba.”

28. Magabta suna cikin Ayiyat! Sun bi ta Migron! Sun bar kayayyakinsu a Mikmash!

29. Sun ƙetare hanya suka kwana a Geba! Mutanen Rama suka firgita. Mutanen da suke cikin Gibeya, garin sarki Saul, sun gudu.

30. Ku yi ihu, ku mutanen Gallim! Ku kasa kunne, ku mutanen Layish! Ku amsa, ku mutanen Anatot!

31. Jama'ar Madmena da na Gebim suna gudu su tsira da rayukansu.

32. Yau abokan gāba suna cikin Nob, daga can suke nuna wa Dutsen Sihiyona yatsa, wato wanda yake cikin Urushalima.

Karanta cikakken babi Ish 10