Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 10:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Kun shiga uku! Kuna kafa dokokin rashin gaskiya don ku zalunci jama'ata.

2. Ta haka kuke hana wa talakawa hakkinsu, kuna kuma ƙin yi musu shari'ar gaskiya. Ta haka kuke ƙwace dukiyar gwauraye, wato matan da mazansu suka rasu, da ta marayu.

3. Me za ku yi sa'ad Allah zai hukunta ku? Me za ku yi kuma sa'ad da ya kawo muku masifa daga wata ƙasa mai nisa? Ina za ku sheƙa neman taimako? A ina kuma za ku ɓoye dukiyarku?

4. Za a kashe ku a yaƙi, ko a kwashe ku, kamammun yaƙi. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.

5. Ubangiji ya ce, “Assuriya! Ina yin amfani da Assuriya kamar kulki don in hukunta waɗanda nake fushi da su.

6. Na aiki Assuriya ta faɗa wa al'ummar da ba ta tsoron Allah, da yaƙi, wato jama'ar da ta sa na yi fushi. Na aike su su yi waso su yi sata, su tattake jama'a kamar ƙura a tituna.”

7. Amma Sarkin Assuriya yana da nasa mugayen shirye-shirye da zai yi. Ya yi niyya ya hallaka al'ummai masu yawa.

8. Ya yi kurari, ya ce, “Kowane shugaban mayaƙana sarki ne!

9. Na ci biranen Kalno da na Karkemish. Na ci biranen Hamat da na Arfad. Na kuma ci Samariya da Dimashƙu.

10. Na miƙa hannuna don in hukunta wa waɗannan mulkoki masu bauta wa gumaka, wato gumakan sun yi yawa fiye da na Urushalima, da na Samariya.

11. Na hallaka Samariya da dukan gumakanta, haka ma zan yi wa Urushalima da siffofin da suke yi wa sujada a can.”

Karanta cikakken babi Ish 10