Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 1:4-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. An hallaka ki, ke al'umma mai zunubi, ku lalatattun mutane! Zunubinku ya ja ku ƙasa! Kun ƙi Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, kun juya masa baya.

5. Me ya sa kuke ta tayarwa? Kuna so a ƙara muku hukunci ne? Ya Isra'ila, kanki duka rauni ne, zuciyarki da kwanyarki suna ciwo.

6. Daga kanki har zuwa ƙafafunki, ba inda yake da lafiya a jikinki. Raunuka da ƙujewa da manyan gyambuna sun rufe jikinki, ba a tsabtace raunukanki an ɗaure ba. Ba a yi musu magani ba.

7. An lalatar da ƙasarku, an ƙone biranenku ƙurmus. Kuna gani, baƙi suka ƙwace ƙasarku, suka mai da ko'ina kufai.

8. Urushalima kaɗai ta ragu, birnin da aka kewaye da yaƙi, ba wata kariya kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi, ko ta mai ƙumu a gonar kankana.

9. Da a ce Ubangiji Mai Runduna bai rage sauran jama'a ba, da an hallakar da Urushalima gaba ɗaya, kamar yadda aka yi wa Saduma da Gwamrata.

10. Ya Urushalima sarakunanki da jama'arki sun zama kamar Saduma da Gwamrata. Ku kasa kunne ga abin da Ubangiji yake faɗa muku. Ku mai da hankali ga abin da Allahnmu yake koya muku.

11. Ya ce, “Kuna tsammani ina jin daɗin dukan hadayun nan da kuke ta miƙa mini? Tumakin da kuke miƙawa hadaya ta ƙonawa, da kitsen kyawawan dabbobinku ya ishe ni. Na gaji da jinin bijimai, da na tumaki, da na awaki.

12. Wa ya roƙe ku ku kawo mini dukan wannan sa'ad da kuka zo yi mini sujada? Wa kuma ya roƙe ku ku yi ta kai da kawowa a kewaye da Haikalina?

13. Ko kusa ba na bukatar hadayunku marasa amfani. Ina jin ƙyamar ƙanshin turaren da kuke miƙawa. Ba zan jure da bukukuwanku na amaryar wata, da na ranakun Asabar, da taronku na addini ba, duka sun ɓaci saboda zunubanku.

14. Ina ƙin bukukuwanku na amaryar wata, da na tsarkakan ranaku. Sun zama nawaya wadda na gaji da ita.

15. “Sa'ad da kuke ɗaga hannuwanku wajen yin addu'a, ba zan dube ku ba. Kome yawan addu'ar da kuka yi, ba zan kasa kunne ba domin zunubi ya ɓata hannuwanku.

Karanta cikakken babi Ish 1