Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 9:10-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Zan yi kuka in yi kururuwa sabodatsaunuka,Zan yi kuka saboda wuraren kiwo,Domin sun bushe sun zama marasaamfani.Ba wanda yake bi ta cikinsu.Ba a kuma jin kukan shanu,Tsuntsaye da namomin jeji, sun gudusun tafi.

11. “Ni Ubangiji na ce, zan mai daUrushalima tsibin kufai,Wurin zaman diloli,Zan kuma mai da biranen Yahuzakufai, inda ba kowa.”

12. Wa yake da isasshiyar hikimar da zai fahimci wannan? Wa Ubangiji ya faɗa masa don ya sanar? Me ya sa ƙasar ta lalace ta zama kufai, har ba wanda yake iya ratsa ta, kamar hamada?

13. Sai Ubangiji ya ce, “Saboda sun bar dokata wadda na sa a gabansu, ba su yi biyayya da maganata ko su yi aiki da ita ba.

14. Amma suka taurare, suka biye wa zuciyarsu, suka bi Ba'al, kamar yadda kakanninsu suka koya musu.

15. Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan ciyar da mutanen nan da abinci mai ɗaci, in shayar da su da ruwan dafi.

16. Zan watsa su cikin sauran al'umma waɗanda su da kakanninsu ba su san su ba, zan sa takobi ya bi su don in hallaka su.

17. “Haka ni Ubangiji Mai Runduna nace,Ku yi tunani, ku kirawo mata masumakoki su zo,Ku aika wa gwanaye fa.”

18. Jama'a suka ce,“Su gaggauta, su ta da murya,Su yi mana kuka da ƙarfi,Har idanunmu su cika da hawaye,Giranmu kuma su jiƙe sharaf.

19. “Gama ana jin muryar kuka dagaSihiyona cewa,‘Ga yadda muka lalace! Aka kunyatarda mu ɗungum!Don mun bar ƙasar, domin sunrurrushe wuraren zamanmu.’ ”

20. Irmiya ya ce,“Ya ku mata, ku ji maganarUbangiji,Ku kasa kunne ga maganar da yafaɗa,Ku koya wa 'ya'yanku mata kukanmakoki,Kowacce ta koya wa maƙwabciyartawaƙar makoki,

21. Gama mutuwa ta shiga tagoginmu,Ta shiga cikin fādodinmu,Ta karkashe yara a tituna,Ta kuma karkashe samari a dandali.

22. Ubangiji ya ce mini,‘Ka yi magana, cewa gawawwakinmutane za su fāɗi tuliKamar juji a saura,Kamar dammunan da masu girbisuka ɗaura,Ba wanda zai tattara su.’ ”

23. Ubangiji ya ce, “Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa, kada mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa, kada kuma mawadaci ya yi fariya da wadatarsa.

24. Amma bari wanda zai yi fariya, ya yi fariya a kan cewa ya fahimce ni, ya kuma san ni. Ni ne Ubangiji mai yin alheri, da gaskiya, da adalci a duniya, gama ina murna da waɗannan abubuwa, ni Ubangiji na faɗa.”

25. Ubangiji ya ce, “Kwanaki suna zuwa sa'ad da zan hukunta dukan waɗanda aka yi musu kaciya,

Karanta cikakken babi Irm 9