Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 6:10-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Da wa zan yi magana don in faɗakarda shi, don su ji?Ga shi, kunnuwansu a toshe suke, suji,Ga shi, maganar Ubangiji kuwa tazama abin ba'a a gare su,Ba su marmarinta.

11-12. Don haka ina cike da fushinUbangijiNa gaji da kannewa.Ubangiji ya ce,“Zan kwararo fushi kan yara da suke atiti.Da kuma kan tattaruwar samari.Za a ɗauke mata da miji duka biyu,Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufatukub-tukub.Za a ba waɗansu gidajensu, dagonakinsu, da matansu,Gama zan nuna ikona in hukuntamazaunan ƙasar.

13. Gama daga ƙaraminsu zuwa babba,Kowannensu yana haɗama ya ciƙazamar riba,Har annabawa da firistoci,Kowannensu ya shiga aikata rashingaskiya.

14. Sun warkar da raunin mutanenasama sama,Suna cewa, ‘Lafiya, Lafiya,’ alhalikuwa ba lafiya.

15. Sun ji kunya sa'ad da suka aikataabubuwan banƙyama?Ba su ji kunya ba ko kaɗan.Ko gezau ba su yi ba,Don haka za su fāɗi tare dafāɗaɗɗu,Sa'ad da na hukunta su, za ahamɓarar da su.Ni Ubangiji na faɗa.”

16. Haka Ubangiji ya ce,“Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba,Ku nemi hanyoyin dā, inda hanyamai kyau take,Ku bi ta, don ku hutar darayukanku.Amma suka ce, ‘Ai, ba za mu bi ta ba.’

17. Na sa muku matsara cewa, in kun jian busa ƙaho ku kula!Amma suka ce, ‘Ba za mu kula ba.’

Karanta cikakken babi Irm 6