Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 50:15-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ku kewaye ta da kuwwar yaƙi!Ta ba da gari,Ginshiƙanta sun fāɗi.An rushe garunta,Gama wannan sakayya ce taUbangiji.Ku sāka mata, ku yi mata kamaryadda ta yi.

16. Ku datse wa Babila mai shuka,Da mai yanka da lauje a lokacingirbi.Saboda takobin azzalumi,Kowa zai koma wurin mutanensa,Kowa kuma zai gudu zuwaƙasarsa.”

17. “Isra'ilawa kamar tumaki ne waɗanda zakuna suka bi su suna kora. Da farko dai Sarkin Assuriya ne ya cinye su. Yanzu kuwa Sarkin Babila, wato Nebukadnezzar, shi ne yake gaigayi ƙasusuwansu.

18. Saboda haka ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila na ce, zan yi wa Sarkin Babila da ƙasarsa hukunci, kamar yadda na hukunta Sarkin Assuriya.

19. Zan komar da Isra'ila a makiyayarsa, zai yi kiwo a Karmel da Bashan. Zai sami biyan bukatarsa a tsaunukan Ifraimu da na Gileyad.

20. Ni Ubangiji na ce sa'ad da lokacin nan ya yi za a nemi laifi da zunubi a cikin Isra'ila da Yahuza, amma ba za a samu ba, gama zan gafarta wa sauran da suka ragu.

21. “Ku haura ku fāɗa wa ƙasarMeratayim da mazaunan Fekod.Ku kashe, ku hallaka su sarai,Ku aikata dukan abin da na umarceku,Ni Ubangiji na faɗa.

22. Hargowar yaƙi tana cikin ƙasar,Da kuma babbar hallakarwa!

23. Ga yadda aka karya gudumar dukanduniya!Ga yadda Babila ta zama abarƙyama ga sauran al'umma!

24. Na kafa miki tarko, ya kuwa kamaki, ya Babila,Ke kuwa ba ki sani ba.An same ki, an kama,Domin kin yi gāba da ni.”

25. Ubangiji ya buɗe taskarmakamansa,Ya fito da makaman hasalarsa,Gama Ubangiji Allah Mai Rundunayana da aikin da zai yi a ƙasarKaldiyawa.

26. Ku zo, ku fāɗa mata daga kowanesashi.Ku buɗe rumbunanta,Ku tsittsiba ta kamar tsibin hatsi,Ku hallakar da ita ɗungum,Kada wani abu nata ya ragu.

Karanta cikakken babi Irm 50