Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 5:4-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sai na ce,“Waɗannan mutane ba su da kirki,Ba su da hankali,Ba su san hanyar Ubangiji,Ko shari'ar Allahnsu ba.

5. Zan tafi wurin manyan mutane, in yimusu magana,Gama sun san nufin Ubangiji, dashari'ar Allahnsu.”Amma dukansu sun ƙi yardaUbangiji ya mallake su,Suka ƙi yi masa biyayya.

6. Domin haka zaki daga kurmi zaikashe su,Kyarkeci kuma daga hamada zaihallaka su.Damisa tana yi wa biranensukwanto,Duk wanda ya fita daga cikinsu sai ayayyage shi,Domin laifofinsu sun yi yawa,Karkacewarsu babba ce.

7. “Don me zan gafarce ki?'Ya'yanki sun rabu da ni,Sun yi rantsuwa da gumaka,Na ciyar da su har sun ƙoshi sosai,Suka yi karuwanci, suka ɗungumazuwa gidajen karuwai,

8. Kamar ƙosassun ingarmu suke,masu jaraba,Kowa yana haniniya, yana nemanmatar maƙwabcinsa.

9. Ba zan hore su saboda waɗannanabubuwa ba?Ni Ubangiji na ce, ba zan ɗauka wakaina fansa a kan wannanal'umma ba?

10. Ku haura, ku lalatar da gonarkurangar inabinta,Amma kada ku yi mata ƙarƙaf,Ku sassare rassanta,Gama su ba na Ubangiji ba ne.

11. Gama mutanen Isra'ila da mutanenYahuzaSun zama marasa aminci a gare ni.Ni Ubangiji na faɗa.”

Karanta cikakken babi Irm 5