Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 5:18-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. “Amma ko a cikin waɗancan kwanaki ba zan yi muku ƙaƙaf ba,” in ji Ubangiji.

19. “Sa'ad da mutanenki suka ce, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi mana waɗannan abubuwa duka?’ sai ki ce musu, ‘Kamar yadda kuka rabu da ni kuka bauta wa gumaka a ƙasarku, haka kuma za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’ ”

20. “Ka sanar wa zuriyar Yakubu dawannan,Ka kuma yi shelarsa a Yahuza, kace,

21. ‘Ku ji wannan, ya ku wawaye,marasa hankali,Kuna da idanu, amma ba ku gani,Kuna da kunnuwa, amma ba kuji.’ ”

22. Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsoronaba?Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba?Ni ne na sa yashi ya zama iyakarteku,Tabbatacciyar iyaka, wadda ba tahayuwa,Ko da yake raƙuman ruwa za su yihauka, ba za su iya haye ta ba,Ko da suna ruri, ba za su iya wuce taba.

23. Amma mutanen nan suna da taurinzuciya, masu halin tayarwa ne,Sun rabu da ni, sun yi tafiyarsu.

24. A zuciya ba su cewa,‘Bari mu ji tsoron UbangijiAllahnmuWanda yake ba mu ruwan sama akan kari,Na kaka da na bazara,Wanda yake ba mu lokacin girbi.’

25. Laifofinku sun raba ku da waɗannanabubuwa.Zunubanku kuma sun hana kusamun alheri.

Karanta cikakken babi Irm 5