Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 5:14-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Saboda haka Ubangiji Allah MaiRunduna ya ce,“Domin sun hurta wannan magana,Ga shi, zan sa maganata a bakinka tazama wuta,Waɗannan mutane kuwa su zamaitace,Wutar za ta cinye su.

15. “Ya ku mutanen Isra'ila, ga shi, inakawo mukuWata al'umma daga nesa,” in jiUbangiji,“Al'umma ce mai ƙarfin hali ta tunzamanin dā.Al'umma wadda ba ku san harshentaba,Ba za ku fahimci abin da suke faɗaba.

16. Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabarine,Dukansu jarumawa ne.

17. Za su cinye amfanin gonakinku daabincinku.Za su ƙare 'ya'yanku mata da maza.Za su cinye garkunanku na tumaki,da na awaki, da na shanu,Za su kuma cinye 'ya'yan inabinkuda na ɓaurenku.Za su hallaka biranenku masu kagarada takobi, waɗanda kuke fariya dasu.

18. “Amma ko a cikin waɗancan kwanaki ba zan yi muku ƙaƙaf ba,” in ji Ubangiji.

19. “Sa'ad da mutanenki suka ce, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi mana waɗannan abubuwa duka?’ sai ki ce musu, ‘Kamar yadda kuka rabu da ni kuka bauta wa gumaka a ƙasarku, haka kuma za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’ ”

20. “Ka sanar wa zuriyar Yakubu dawannan,Ka kuma yi shelarsa a Yahuza, kace,

21. ‘Ku ji wannan, ya ku wawaye,marasa hankali,Kuna da idanu, amma ba ku gani,Kuna da kunnuwa, amma ba kuji.’ ”

22. Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsoronaba?Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba?Ni ne na sa yashi ya zama iyakarteku,Tabbatacciyar iyaka, wadda ba tahayuwa,Ko da yake raƙuman ruwa za su yihauka, ba za su iya haye ta ba,Ko da suna ruri, ba za su iya wuce taba.

Karanta cikakken babi Irm 5