Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 41:12-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. sai suka kwashe mutanensu duka, suka tafi su yi yaƙi da Isma'ilu ɗan Netaniya. Suka iske shi a babban tafkin da take a Gibeyon.

13. Sa'ad da dukan jama'ar da Isma'ilu ya kwashe suka ga Yohenan ɗan Kareya, da dukan shugabannin sojoji tare da shi, sai suka yi murna.

14. Dukan mutanen nan da Isma'ilu ya kwashe su ganima daga Mizfa, suka juya, suka koma wurin Yohenan ɗan Kareya.

15. Amma Isma'ilu ɗan Netaniya tare da mutum takwas suka tsere suka gudu zuwa wurin Ammonawa.

16. Sai Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji da suke tare da shi, suka kwashe dukan sauran jama'a, waɗanda Isma'ilu ɗan Netaniya ya kamo daga Mizfa bayan ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wato sojoji da mata, da yara, da bābāni, su ne Yohenan ya komo da su daga Gibeyon.

17. Suka fa tafi suka zauna a wurin Kimham kusa da Baitalami. Suna nufin su tafi Masar,

18. don gudun Kaldiyawa, gama suna jin tsoronsu, domin Isma'ilu ɗan Netaniya ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam wanda Sarkin Babila ya naɗa shi mai mulkin ƙasa.

Karanta cikakken babi Irm 41