Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 4:2-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Idan kun yi rantsuwa kuka ce,‘Har da ran Ubangiji kuwa,‘Da gaskiya, da aminci, da adalci,Sa'an nan sauran al'umma za su soin sa musu albarka,Za su kuma yabe ni.”

3. Ubangiji ya ce wa mutanen Yahuza da na Urushalima,“Ku kafce saurukanku,Kada ku yi shuka cikin ƙayayuwa.

4. Ya ku mutanen Yahuza da naUrushalima,Ku yi wa kanku kaciya dominUbangiji,Ku kawar da loɓar zukatankuDon kada fushina ya fito kamarwuta,Ya cinye, ba mai iya kashewa,Saboda mugayen ayyukan da kukaaikata.”

5. “Ku yi shela a cikin Yahuza,Ku ta da murya a Urushalima, kuce,‘Ku busa ƙaho a dukan ƙasar!’Ku ta da murya da ƙarfi, ku ce,‘Ku tattaru, mu shiga birane masugaru.’

6. Ku ta da tuta wajen Sihiyona!Ku sheƙa a guje neman mafaka,kada ku tsaya!Gama zan kawo masifa da babbarhalaka daga arewa.

Karanta cikakken babi Irm 4