Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 38:11-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Sai Ebed-melek ya tafi da mutanen, ya kuma tafi gidan sarki, a ɗakin ajiya, ya kwaso tsummoki da tsofaffin tufafi, ya zurara wa Irmiya a rijiyar.

12. Ebedmelek, mutumin Habasha, ya ce wa Irmiya ya sa tsummokin da tsofaffin tufafin a hammatarsa, ya zarga igiya, Irmiya kuwa ya yi yadda aka ce masa.

13. Suka jawo Irmiya da igiyoyi, suka fito da shi daga rijiya. Irmiya kuwa ya zauna a gidan waƙafi.

14. Sarki Zadakiya ya aika a kirawo annabi Irmiya. Ya tafi ya sadu da Irmiya a ƙofa ta uku ta Haikalin Ubangiji. Sarki kuwa ya ce wa Irmiya, “Zan yi maka tambaya, kada kuwa ka ɓoye mini kome.”

15. Irmiya kuwa ya ce wa Zadakiya, “Idan na faɗa maka gaskiya za ka kashe ni, idan kuma na ba ka shawara, ba za ka karɓi shawarata ba.”

16. Sarki Zadakiya ya rantse wa Irmiya a ɓoye, ya ce, “Na rantse da Ubangiji, wanda yake ba mu rai, ba zan kashe ka ko in bashe ka a hannun waɗannan mutane da suke neman ranka ba.”

17. Irmiya ya ce wa Zadakiya, “Haka Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, idan ka miƙa wuya ga sarakunan Sarkin Babila, za ka tsira, ba kuwa za a ƙone birnin da wuta ba, kai da gidanka za ku tsira.

18. Amma idan ba ka miƙa wuya ga sarakunan Sarkin Babila ba, to, za a ba da wannan birni a hannun Kaldiyawa, za su ƙone shi da wuta. Kai kuma ba za ka tsira daga hannunsu ba.”

Karanta cikakken babi Irm 38