Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 33:16-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. A waɗannan kwanaki za a ceci mutanen Yahuza, mutanen Urushalima kuwa za su zauna lafiya. Sunan da za su sa wa Urushalima birninsu, shi ne, ‘Adalcinmu Ubangiji ne.’

17. Gama ni Ubangiji na ce Dawuda ba zai taɓa rasa mutumin da zai zauna a gadon sarautar Isra'ila ba.

18. Lawiyawa kuma ba za su rasa firistocin da za su tsaya a gabana, suna miƙa hadayun ƙonawa ba, da hadayu na gari na ƙonawa, su kuma miƙa sadaka har abada.”

19. Ubangiji kuma ya yi magana da Irmiya ya ce, “Haka Ubangiji ya faɗa,

20. idan ka iya hana dare da yini su bayyana a ƙayyadaddun lokatansu,

21. to, ashe, alkawarin da na yi wa bawana Dawuda zai tashi ke nan, har ya rasa ɗan da zai yi mulki a gadon sarautarsa, alkawarin kuma da na yi wa firistoci masu yi mini hidima, da ma'aikatana, zai tashi.

22. Kamar yadda ba a iya ƙidaya rundunan sammai ba, ba a iya kuma auna yashin teku ba, haka nan zan yawaita zuriyar bawana Dawuda da Lawiyawa, firistoci, masu yi mini hidima.”

23. Ubangiji kuma ya ce wa Irmiya,

24. “Ba ka ji abin da mutanen nan suke cewa ba? Wai, ‘Ubangiji ya ƙi iyalin nan biyu da ya zaɓa!’ Suka raina jama'ata, ba su kuma maishe ta al'umma ba.

25. Amma ni Ubangiji na ce, idan ban kafa alkawarina game da yini, da kuma game da dare, da ka'idodin da take mulkin sammai da duniya ba,

26. sa'an nan zan ƙi zuriyar Yakubu da bawana Dawuda. Ba kuma zan zaɓi wani daga cikin zuriyarsa ya yi mulkin zuriyar Ibrahim, da ta Ishaku, da ta Yakubu ba. Amma zan mayar musu da arzikinsu, in nuna jinƙai a kansu.”

Karanta cikakken babi Irm 33