Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 33:12-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Wannan wuri wanda yake kufai, inda ba mutum ko dabba, da cikin dukan biranensa, zai sāke zama makiyaya, inda masu kiwo za su zauna da garkunansu.

13. A garuruwan ƙasar tuddai, da na kwaruruka, da na Negeb, da na ƙasar Biliyaminu, da na wuraren da suke kewaye da Urushalima, da na Yahuza, garkuna za su sāke bi ta ƙarƙashin hannun mai ƙidayawa,” in ji Ubangiji.

14. “Ga shi, kwanaki suna zuwa sa'ad da zan cika alkawarin da na yi wa mutanen Isra'ila da na Yahuza.

15. A waɗannan kwanaki da a lokacin nan, zan sa wani reshe mai adalci ya fito daga zuriyar Dawuda, zai aikata gaskiya da adalci a ƙasar.

16. A waɗannan kwanaki za a ceci mutanen Yahuza, mutanen Urushalima kuwa za su zauna lafiya. Sunan da za su sa wa Urushalima birninsu, shi ne, ‘Adalcinmu Ubangiji ne.’

17. Gama ni Ubangiji na ce Dawuda ba zai taɓa rasa mutumin da zai zauna a gadon sarautar Isra'ila ba.

18. Lawiyawa kuma ba za su rasa firistocin da za su tsaya a gabana, suna miƙa hadayun ƙonawa ba, da hadayu na gari na ƙonawa, su kuma miƙa sadaka har abada.”

19. Ubangiji kuma ya yi magana da Irmiya ya ce, “Haka Ubangiji ya faɗa,

20. idan ka iya hana dare da yini su bayyana a ƙayyadaddun lokatansu,

21. to, ashe, alkawarin da na yi wa bawana Dawuda zai tashi ke nan, har ya rasa ɗan da zai yi mulki a gadon sarautarsa, alkawarin kuma da na yi wa firistoci masu yi mini hidima, da ma'aikatana, zai tashi.

22. Kamar yadda ba a iya ƙidaya rundunan sammai ba, ba a iya kuma auna yashin teku ba, haka nan zan yawaita zuriyar bawana Dawuda da Lawiyawa, firistoci, masu yi mini hidima.”

23. Ubangiji kuma ya ce wa Irmiya,

24. “Ba ka ji abin da mutanen nan suke cewa ba? Wai, ‘Ubangiji ya ƙi iyalin nan biyu da ya zaɓa!’ Suka raina jama'ata, ba su kuma maishe ta al'umma ba.

Karanta cikakken babi Irm 33