Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 32:14-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, ‘Ka ɗauki waɗannan takardun shaida, wadda aka liƙe da wadda ba a liƙe ba, ka sa su a cikin tukunyar ƙasa domin kada su lalace.’

15. Gama haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa, ‘Gidaje, da gonaki, da gonakin inabi, za a sāke sayensu a ƙasan nan.’ ”

16. Bayan da na ba Baruk, ɗan Neriya, takardar sharuɗan ciniki, sai na yi addu'a ga Ubangiji, na ce,

17. “Ya Ubangiji Allah, kai ne ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka da ƙarfinka, ba abin da ya fi ƙarfinka.

18. Kakan nuna madawwamiyar ƙauna ga dubbai, amma kakan hukunta wa 'ya'ya saboda laifin ubanninsu. Ya maigirma Maɗaukaki, Allah, sunanka kuwa Ubangiji Mai Runduna.

19. Kai babban mashawarci ne, mai aikata manyan ayyukanka. Kana ganin dukan ayyukan 'yan adam. Kakan sāka wa kowa bisa ga halinsa da ayyukansa.

20. Ka aikata alamu da al'ajabai a ƙasar Masar. Har wa yau kuma kana aikata su a Isra'ila da kuma cikin dukan al'ummai, ka yi wa kanka suna kamar yadda yake a yau.

21. Ta wurin alamu da al'ajabai, da iko, da ƙarfi, da banrazana, ka fito da jama'arka Isra'ila daga ƙasar Masar.

22. Ka kuwa ba su wannan ƙasa wadda ka rantse za ka ba kakanninsu. Ƙasar da take cike da yalwar albarka.

23. Amma sa'ad da suka shiga cikinta suka mallake ta, ba su yi biyayya da muryarka ba, ba su kiyaye dokokinka ba, ba su aikata dukan abin da ka umarce su ba, saboda haka ka sa wannan masifa ta auko musu.

24. “Ga shi, Kaldiyawa sun gina mahaurai kewaye da birnin da suka kewaye shi da yaƙi. Saboda takobi, da yunwa, da annoba aka ba da birnin a hannun Kaldiyawa, waɗanda suke yaƙi da birnin. Abin da ka faɗa ya tabbata, ka kuwa gani.

25. Duk da haka ya Ubangiji Allah, ka ce mini, ‘Sayi gonar da kuɗi, a gaban shaidu, ko da yake an ba da birnin a hannun Kaldiyawa.’ ”

26. Ubangiji kuwa ya ce wa Irmiya,

27. “Ni ne Ubangiji Allah na dukan 'yan adam, ba abin da ya fi ƙarfina.

Karanta cikakken babi Irm 32