Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 31:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce, “Lokaci yana zuwa da zan zama Allah na dukan iyalan Isra'ila, za su kuwa zama jama'ata.”

2. Haka Ubangiji ya ce, “Jama'ar dasuka tsere wa takobi,Sun sami alheri a cikin jeji,A sa'ad da Isra'ila suka nemihutawa.”

3-4. Ubangiji ya bayyana gare ni tundaga nesa cewa,“Ya Isra'ila, budurwa!Na kusace ki da madawwamiyarƙaunata,Ba zan fasa amintacciyar ƙaunata agare ki ba.Zan sāke gina ki,Za ki kuwa ginu,Za ki ɗauki kayan kaɗe-kaɗe,Za ki shiga rawar masu murna.

5. Za ki sāke dasa gonar inabiA kan duwatsun Samariya,Masu dashe za su dasa,Za su mori 'ya'yan.

6. Gama rana tana zuwa sa'ad da maitsaro zai yi kiraA ƙasar tudu ta Ifraimu, ya ce,‘Ku tashi mu haura zuwa SihiyonaZuwa wurin Ubangiji Allahnmu.’ ”

7. Ga abin da Ubangiji ya ce,“Raira wa Yakubu waƙar farin cikida ƙarfi,Ku ta da murya saboda shugabanal'ummai,Ku yi shela, ku yi yabo, ku ce,‘Ya Ubangiji ka ceci jama'arka,Wato ringin mutanen Isra'ila,’

8. Ga shi, zan fito da su daga ƙasararewa,Zan tattaro su daga manisantanwurare na duniya,Tare da su makafi da guragu,Da mace mai goyo da mai naƙuda,Za su komo nan a babbar ƙungiya.

Karanta cikakken babi Irm 31