Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 3:12-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ya ce mini in tafi wajen arewa in yi shela in ce,“Ki komo ya Isra'ila, marar aminci,Ni Ubangiji, na faɗa.Domin ni mai jinƙai ne,Ba zan yi fushi da ke ba.Ba zan yi fushi da ke har abada ba,Ni, Ubangiji na faɗa.

13. Ke dai ki yarda da laifinki,Da kika yi wa Ubangiji Allahnki,Kin kuma watsar da mutuncinki awurin baƙiA gindin kowane itace mai duhuwa.Kika ƙi yin biyayya da maganata,Ni, Ubangiji, na faɗa.

14. “Ku komo, ya ku mutane marasaaminci,Gama ni ne Ubangijinku.Zan ɗauki mutum guda daga kowanegari,In ɗauki mutum biyu daga kowaneiyali,Zan komo da su zuwa DutsenSihiyona.

15. Zan ba ku sarakuna waɗanda suke yi mini biyayya da hikima da fahimi.

16. Sa'ad da kuka yawaita a ƙasar, mutane ba za su ƙara yin magana a kan akwatin alkawari na Ubangiji ba. Ba za su ƙara yin tunaninsa ko su tuna da shi, ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba.

17. In lokacin nan ya yi, za a kira Urushalima gadon sarautar Ubangiji, dukan sauran a'umma za su taru a Urushalima da sunana. Ba za su ƙara bin tattaurar zuciyarsu mai mugunta ba.

18. A waɗannan kwanaki mutanen Yahuza za su haɗu da mutanen Isra'ila. Tare za su zo daga ƙasar arewa zuwa cikin ƙasar da na ba kakanninku gādo.”

19. “Isra'ila, na yi niyya in karɓe kukamar ɗana,In gādar muku da kyakkyawarƙasaMafi kyau a dukan duniya.Na zaci za ku ce ni ne mahaifinku,Ba za ku ƙara rabuwa da bina ba.

20. Hakika kamar yadda mace mararaminci takan bar mijinta,Haka kun zama marar aminci a gareni, ya jama'ar Isra'ila.Ni Ubangiji, na faɗa.”

21. An ji murya a kan filayen tuddai,Kūka da roƙo ne na 'ya'yanIsra'ila maza,Domin sun rabu da hanyarsu,Sun manta da Ubangiji Allahnsu.

22. “Ku juyo ku marasa aminci,Zan warkar da rashin amincinku.”“To, ga shi, mun zo gare ka,Gama kai ne Ubangiji Allahnmu,

23. Daga kan tuddai ba mu da wanitaimako,Ko daga hayaniyar da ake yi a kanduwatsu,Daga wurin Ubangiji Allahnmu nekaɗai taimakon Isra'ila yakefitowa.

Karanta cikakken babi Irm 3