Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 3:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce,“Idan mutum ya saki matarsa,Ta kuwa rabu da shi, har ta auriwani,Ya iya ya komo da ita?Ashe, yin haka ba zai ƙazantar daƙasar ba?Ya Isra'ila, kin yi karuwanci,Abokan sha'anin karuwancinki, sunada yawa.Za ki sāke komowa wurina?Ni, Ubangiji, na faɗa.

2. Ki ta da idonki, ki duba filayentuddai ki gani,Akwai wurin da ba ki laɓe kin yikaruwanci ba?Kin yi ta jiran abokan sha'aninkaruwancinki a kan hanya,Kamar Balaraben da yake fako ahamada.Kin ƙazantar da ƙasar da mugunkaruwancinki.

3. Saboda haka aka ƙi yin ruwa,Ruwan bazara bai samu ba.Goshinki irin na karuwa ne, ba ki jinkunya.

4. “Yanzu kin ce, ‘Kai ne mahaifina,Ka ƙaunace ni tun ina cikinƙuruciyata.

5. Za ka dinga yin fushi da ni?Za ka husata da ni har abada?’Ga shi, ke kika faɗa, amma ga shi,kin aikata dukan muguntar dakika iya yi.”

6. A zamanin sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da take yi, ita marar amincin nan, wato Isra'ila? Yadda a kowane tudu mai tsayi, da a gindin kowane itace mai duhuwa, a wurare ne ta yi karuwancinta.

7. Na yi zaton bayan da ta aikata wannan duka, za ta komo wurina. Amma ba ta komo ba, maƙaryaciyar 'yar'uwarta, wato Yahuza, ta gani.

8. Yahuza kuwa ta ga dukan karuwancin da marar amincin nan, Isra'ila ta yi, na sake ta, na ba ta takardar sarki. Amma duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza, ba ta ji tsoro ba, amma ita ma ta tafi ta yi karuwanci.

9. Domin karuwanci a wurinta abu ne mai sauƙi, ta ƙazantar da ƙasar. Ta yi karuwanci da duwatsu, da itatuwa.

10. Duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza ba ta juyo wurina da zuciya ɗaya ba, sai a munafunce, ni Ubangiji na faɗa.”

11. Ubangiji kuma ya faɗa mini, ko da yake Isra'ila ta bar binsa, duk da haka ta nuna laifinta bai kai na Yahuza marar aminci ba.

12. Ya ce mini in tafi wajen arewa in yi shela in ce,“Ki komo ya Isra'ila, marar aminci,Ni Ubangiji, na faɗa.Domin ni mai jinƙai ne,Ba zan yi fushi da ke ba.Ba zan yi fushi da ke har abada ba,Ni, Ubangiji na faɗa.

13. Ke dai ki yarda da laifinki,Da kika yi wa Ubangiji Allahnki,Kin kuma watsar da mutuncinki awurin baƙiA gindin kowane itace mai duhuwa.Kika ƙi yin biyayya da maganata,Ni, Ubangiji, na faɗa.

14. “Ku komo, ya ku mutane marasaaminci,Gama ni ne Ubangijinku.Zan ɗauki mutum guda daga kowanegari,In ɗauki mutum biyu daga kowaneiyali,Zan komo da su zuwa DutsenSihiyona.

15. Zan ba ku sarakuna waɗanda suke yi mini biyayya da hikima da fahimi.

Karanta cikakken babi Irm 3