Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 29:22-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Saboda su duka waɗanda aka kai bautar talala daga Yahuza zuwa Babila, za su mori kalman nan suna yin la'ana cewa, “Ubangiji ya maishe ka kamar Zadakiya da Ahab, waɗanda Sarkin Babila ya gasa da wuta!”

23. Gama sun yi wauta a Isra'ila, sun yi zina da matan maƙwabtansu, sun yi ƙarya da sunana, ni kuwa ban umarce su ba. Ni na sani, ni ne kuma shaida, ni Ubangiji na faɗa.

24. “Zancen Shemaiya mutumin Nehelam,

25. haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya faɗa. Ga shi, ka aika da wasiƙu da sunanka zuwa ga dukan jama'ar da suke a Urushalima, da zuwa ga Zafaniya ɗan Ma'aseya, firist, da kuma ga dukan firistoci, cewa

26. Ubangiji ya naɗa ka firist a madadin Yehoyada firist, ka lura da Haikalin Ubangiji, ka sa kowane mahaukacin da zai yi annabci a turu, ka sa masa ƙangi.

27. To, me ya sa ba ka tsauta wa Irmiya, mutumin Anatot, wanda yake yin maka annabci ba?

28. Gama ya aiko mana a Babila, cewa za mu daɗe a zaman talala, mu gina wa kanmu gidaje, mu zauna a ciki, mu dasa gonaki mu ci amfaninsu.”

29. Sai Zafaniya firist, ya karanta wasiƙan nan a gaban annabi Irmiya.

30. Ubangiji kuwa ya yi magana da Irmiya, ya ce,

31. ya aika wa dukan waɗanda suke zaman talala ya ce, “Haka Ubangiji ya ce a kan Shemaiya mutumin Nehelam, ‘Saboda Shemaiya ya yi muku annabci, alhali ni ban aike shi ba, ya sa ku dogara ga ƙarya,’

32. saboda haka Ubangiji ya ce, ‘ga shi, zan hukunta Shemaiya, mutumin Nehelam, shi da zuriyarsa ba za a bar masa mai rai ko ɗaya a wannan jama'a ba, wanda zai ga irin alherin da zan yi wa jama'ata, gama ya kuta tayarwa ga Ubangiji,’ ” in ji Ubangiji.

Karanta cikakken babi Irm 29