Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 27:10-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Suna yi muku annabcin ƙarya ne, za su kuwa sa a kai ku wata ƙasa nesa da ƙasarku. Zan kore ku, za ku kuwa lalace.

11. Amma duk al'ummar da za ta ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyanta, ta kuma bauta masa, zan bar ta a ƙasarta, ta yi noman ƙasarta, ta zauna a ciki, ni Ubangiji na faɗa.’ ”

12. Sai na faɗa wa Zadakiya Sarkin Yahuza wannan magana cewa, “Ka ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyanka, ka bauta masa, shi da mutanensa, don ka rayu!

13. Don me kai da mutanenka za ku mutu ta takobi, da yunwa, da annoba, kamar yadda Ubangiji ya yi magana a kan kowace al'umma da ta ƙi ta bauta wa Sarkin Babila?

14. Kada ka kasa kunne ga maganar annabawan da suke ce maka, ‘Ba za ku bauta wa Sarkin Babila ba.’ Annabcin ƙarya suke yi muku.

15. Gama Ubangiji ya ce shi bai aike su ba, annabcin ƙarya suke yi muku da sunansa, don ya kore ku, ku halaka, ku da annabawan da suke yi muku annabci.”

16. Sa'an nan na faɗa wa firistoci da jama'a cewa, “In ji Ubangiji, kada ku kasa kunne ga abin da annabawanku suke muku annabci cewa, ‘Ba da daɗewa ba za a komo da kayan Haikalin Ubangiji daga Babila.’ Ƙarya ce suke yi muku.

17. Kada ku ji su, amma ku bauta wa Sarkin Babila don ku rayu! Don me birnin nan zai zama kufai?

18. Idan su annabawa ne, idan kuwa Ubangiji yana magana da su, to, bari su roƙi Ubangiji Mai Runduna kada a tafi Babila da kayayyakin da suka ragu a Haikalin Ubangiji, da a fādar Sarkin Yahuza, da a Urushalima.

19. Gama Ubangiji Mai Runduna ya faɗi zancen ginshiƙai, da babbar kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan,

Karanta cikakken babi Irm 27