Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 27:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A farkon sarautar Zadakiya ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Ubangiji ya yi wa Irmiya magana.

2. Ya ce ya yi wa kansa karkiyar itace da maɗaurai na fata ya ɗaura su a wuyansa,

3. ya aika da magana zuwa ga Sarkin Edom, da Sarkin Mowab, da Sarkin Ammon, da Sarkin Taya, da Sarkin Sidon ta hannun manzannin da suka zo Urushalima wurin Zadakiya Sarkin Yahuza.

4. Ubangiji ya ce wa Irmiya ya umarce su, su tafi, su faɗa wa iyayengijinsu cewa, “In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ga abin da za ku faɗa wa iyayengijinku,

5. ‘Ni ne da ikona da ƙarfina na yi duniya, da mutane, da dabbobi waɗanda suke cikinta. Nakan ba da ita ga wanda na ga dama.

6. Yanzu fa na ba bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila, dukan ƙasashen nan, na kuma ba shi namomin jeji su bauta masa.

7. Dukan ƙasashe za su bauta masa, da shi da ɗansa, da jikansa, har lokacin da na sa ƙasar ta fāɗi, sa'an nan al'ummai masu yawa da manyan sarakuna za su bautar da shi.

8. “ ‘Amma idan wata al'umma ko wani mulki bai yarda ya bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila ba, bai kuma ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyansa ba, zan hukunta wa wannan al'umma da takobi, da yunwa, da annoba, har in hallaka ta, ta hannun Nebukadnezzar, ni Ubangiji na faɗa.

9. Saboda haka kada ku saurari annabawanku, da masu duba, da masu mafarkai, da matsubbata, ko masu sihiri waɗanda suka ce muku ba za ku bauta wa Sarkin Babila ba.

10. Suna yi muku annabcin ƙarya ne, za su kuwa sa a kai ku wata ƙasa nesa da ƙasarku. Zan kore ku, za ku kuwa lalace.

11. Amma duk al'ummar da za ta ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyanta, ta kuma bauta masa, zan bar ta a ƙasarta, ta yi noman ƙasarta, ta zauna a ciki, ni Ubangiji na faɗa.’ ”

12. Sai na faɗa wa Zadakiya Sarkin Yahuza wannan magana cewa, “Ka ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyanka, ka bauta masa, shi da mutanensa, don ka rayu!

13. Don me kai da mutanenka za ku mutu ta takobi, da yunwa, da annoba, kamar yadda Ubangiji ya yi magana a kan kowace al'umma da ta ƙi ta bauta wa Sarkin Babila?

14. Kada ka kasa kunne ga maganar annabawan da suke ce maka, ‘Ba za ku bauta wa Sarkin Babila ba.’ Annabcin ƙarya suke yi muku.

Karanta cikakken babi Irm 27