Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 26:16-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Sarakuna kuwa da dukan jama'a suka ce wa firistoci da annabawa, “Wannan mutum bai yi abin da ya isa hukuncin kisa ba, gama ya yi magana da sunan Ubangiji Allahnmu.”

17. Sai waɗansu daga cikin dattawan ƙasar suka miƙe tsaye, suka ce wa dukan taron jama'a,

18. “Mika kuwa, mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya faɗa wa dukan mutanen Yahuza cewa,‘Ga abin da Ubangiji Mai Rundunaya ce,Za a nome Sihiyona kamar gona,Urushalima kuwa za ta zama tsibinjuji,Ƙwanƙolin dutsen Haikalin zai zamakurmi.’

19. Ashe, Hezekiya Sarkin Yahuza da dukan Yahuza sun kashe shi ne? Ashe, Hezekiya bai ji tsoron Ubangiji, ya roƙi alherinsa ba? Ashe, Ubangiji bai janye masifar da ya hurta a kansu ba? Yanzu fa gab muke da mu jawo wa kanmu babbar masifa.”

20. Akwai wani mutum kuma wanda ya yi annabci da sunan Ubangiji. Sunansa Uriya ɗan Shemaiya mutumin Kiriyat-yeyarim. Ya yi annabci gāba da birnin nan da ƙasan nan da magana irin ta Irmiya.

Karanta cikakken babi Irm 26