Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 21:10-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Gama na ƙudura zan kawo wa wannan birni masifa, ba alheri ba. Zan bashe shi a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai ƙone shi da wuta.’ ”

11. “Sai ka faɗa wa gidan sarautar Yahuza cewa, ‘Ku ji maganar Ubangiji,

12. Ya gidan Dawuda, ni Ubangiji na ce,Ku aikata adalci kowace safiya.Ku ceci wanda aka yi masa ƙwacedaga hannun mai matsa masa,Don kada hasalata ta tashi kamarwuta,Ta yi ƙuna, har ba mai iya kasheta,Saboda mugayen ayyukanku.

13. Ga shi, ina gāba da ku, ya kumazaunan kwarin,Ya dutsen da yake a fili,’ in jiUbangiji.‘Ku da kuke cewa, wa zai iyagangarowa wurinku,Ko kuwa wa zai shiga wurinzamanku?

14. Zan hukunta ku bisa ga ayyukanku,’in ji Ubangiji,‘Zan sa wa jejin ƙasar wuta.Za ta cinye duk abin da yake kewaye daita.’ ”

Karanta cikakken babi Irm 21