Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 16:12-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ku kuma kun yi laifi fiye da na kakanninku. Kowannenku kuwa ya bi tattauran mugun nufin zuciyarsa, yana ƙin kasa kunne gare ni.

13. Don haka zan fitar da ku daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasa wadda ku ko kakanninku ba ku sani ba. A can za ku bauta wa gumaka dare da rana, gama ba zan nuna muku ƙauna ba.’

14. “Saboda haka, ga shi, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “da ba za a ƙara cewa, ‘Na rantse da ran Ubangiji wanda ya fito da jama'ar Isra'ila daga ƙasar Masar ba.’

15. Amma za a ce, ‘Na rantse da Ubangiji wanda ya fito da jama'ar Isra'ila daga ƙasar arewa, da kuma daga dukan ƙasashe da ya kora su,’ gama zan komo da su zuwa ƙasar da na ba kakanninsu.

16. “Ga shi, ina aiko da masunta da yawa,” in ji Ubangiji, “za su kuwa kama su, daga baya kuma zan aika da mafarauta da yawa, za su farauce su daga kowane tsauni, da tudu, da kogwannin duwatsu.

17. Gama ina ganin dukan ayyukansu, ba a ɓoye suke a gare ni ba, muguntarsu kuma ba a ɓoye take a gare ni ba.

18. Zan riɓaɓɓanya sakayyar da zan yi musu saboda muguntarsu da zunubinsu, domin sun ƙazantar da ƙasata da ƙazantattun gumakansu marasa rai, abin gādona kuma sun cika shi da abubuwansu na banƙyama.”

19. “Ya Ubangiji, ƙarfina da kagarata,Mafakata a ranar wahala,A gare ka al'ummai za su zo,Daga ƙurewar duniya, su ce,‘Kakanninmu ba su gāji kome ba, saiƙarya,Da abubuwan banza marasaamfani.’

20. Mutum zai iya yi wa kansa alloli?Ai, waɗannan ba alloli ba ne!”

21. Ubangiji ya ce,“Saboda haka, ga shi, zan sa su sani,Sau ɗayan nan kaɗai zan sa su su sanikona da ƙarfina,Za su kuma sani sunana Ubangijine.”

Karanta cikakken babi Irm 16