Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 15:9-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ita wadda ta haifi 'ya'ya bakwai tayi yaushi ta suma,Ranarta ta faɗi tun lokaci bai yi ba,An kunyatar da ita, an wulakantarda ita.Waɗanda suka ragu daga cikinsuZan bashe su ga takobi gaban abokangābansu.Ni Ubangiji na faɗa.”

10. Kaitona, ya mahaifiyata, da kika haife ni, mai jayayya mai gardama da kowa cikin dukan ƙasar! Ban ba da rance ba, ba kuma wanda ya ba ni rance, duk da haka dukansu suna zagina.

11. Ubangiji ya ce mini, “Zan keɓe ka domin alheri, hakika zan sa abokan gaba su yi roƙo gare ka a lokacin bala'i da kuma lokacin damuwa.

12. Wa zai iya karya ƙarfe ko tagulla daga arewa?”

13. Ubangiji ya ce mini, “Zan ba da wadatarku da dukiyarku ganima kyauta, saboda dukan zunubanku a dukan ƙasar.

14. Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama fushina ya kama kamar wuta, zai yi ta ci har abada.”

15. Sa'an nan Irmiya ya ce, “YaUbangiji, ka sani.Kai ne, ka ziyarce ni,Ka kuma sāka wa waɗanda suketsananta mini.Ka sani saboda kai nake shan zargi.

16. Maganarka da na samu na ci.Maganarka kuwa ta zama abarmurna a gare ni,Ta faranta mini zuciya.Gama ana kirana da sunanka,Ya Ubangiji Allah Mai Runduna.

17. Ban zauna cikin ƙungiyar masuannashuwa ba.Ban kuwa yi murna ba,Na zauna ni kaɗai saboda kana tareda ni,Gama ka sa na cika da haushi.

18. Me ya sa azabata ta ƙi ƙarewa,Raunukana kuma ba su warkuwa,Sun kuwa ƙi warkewa?Za ka yaudare ni kamar rafi,Ko kamar ruwa mai ƙafewa?”

19. “Domin haka ga abin da ni, Ubangijina ce,Idan ka komo sa'an nan zan kawoka.Za ka tsaya a gabana.Idan ka hurta abin da yake gaskiyaba na ƙarya ba,Za ka zama kakakina.Za su komo gare ka,Amma kai ba za ka koma wurinsuba.

Karanta cikakken babi Irm 15