Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 15:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da a ce Musa da Sama'ila za su tsaya a gabana, duk da haka zuciyata ba za ta komo wurin mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana su yi tafiyarsu!

2. Sa'ad da suka tambaye ka, ‘Ina za mu tafi?’ Sai ka faɗa musu cewa, Ubangiji ya ce,‘Waɗanda suke na annoba, su tafi gaannoba!Waɗanda suke na takobi, su tafi gatakobi!Waɗanda suke na yunwa, su tafi gayunwa!Waɗanda suke na bauta, su tafi gabauta!’

3. Zan sa musu masu hallakarwa huɗu,” in ji Ubangiji, “da takobi don kisa, da karnuka don yayyagawa, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobin duniya don su cinye, su hallakar.

4. Zan kuma sa su zama abin banƙyama ga dukan mulkokin duniya saboda abin da Manassa ɗan Hezekiya, Sarkin Yahuza ya aikata a Urushalima.

5. “Wa zai ji tausayinki, yaUrushalima?Wa zai yi baƙin ciki dominki?Wa kuma zai ratso wurinki don yatambayi lafiyarki?

6. Ni Ubangiji na ce, kun ƙi ni, kuna takomawa da baya,Don haka na nuna ikona gāba da ku,na hallaka ku,Na gaji da jin tausayinku!

7. Na sheƙe su da abin sheƙewa aƙofofin garuruwan ƙasar.Na sa 'ya'yansu su mutu, na hallakamutanena,Ba su daina yin mugayen ayyukansuba.

8. Na yawaita gwauraye, wato mata damazansu suka mutu,Fiye da yashin teku.Na kawo wa uwayen samari maihallakarwa da tsakar rana.Na sa azaba da razana su auka musufarat ɗaya.

9. Ita wadda ta haifi 'ya'ya bakwai tayi yaushi ta suma,Ranarta ta faɗi tun lokaci bai yi ba,An kunyatar da ita, an wulakantarda ita.Waɗanda suka ragu daga cikinsuZan bashe su ga takobi gaban abokangābansu.Ni Ubangiji na faɗa.”

Karanta cikakken babi Irm 15