Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 13:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, ya ce, “Tafi ka sayo lilin na yin ɗamara, ka sha ɗamara da shi kada kuwa ka tsoma shi a ruwa.”

2. Sai na sayo abin ɗamara kamar yadda Ubangiji ya ce, na sha ɗamara da shi.

3. Ubangiji kuma ya sāke yin magana da ni sau na biyu,

4. ya ce, “Ka ɗauki abin ɗamara da ka sayo, wanda ka ɗaura, ka tafi Kogin Yufiretis, ka ɓoye shi a cikin kogon dutse.”

5. Sai na tafi, na ɓoye shi a Yufiretis kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.

6. Bayan an ɗan daɗe, sai Ubangiji ya ce mini, “Tashi, ka tafi Yufiretis, ka ɗauko abin ɗamara wanda na umarce ka ka ɓoye a can.”

7. Sai na tafi Yufiretis, na haƙa na ɗauko abin ɗamara daga wurin da na ɓoye shi. Amma abin ɗamara ya lalace, ba shi da sauran amfani.

8. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

9. “Haka zan lalatar da alfarmar Yahuza da yawan alfarmar Urushalima.

10. Wannan muguwar jama'a, wadda ta ƙi jin maganata, wadda ta taurare, ta bi son zuciyarta, ta kuma bi gumaka ta bauta musu, ta yi musu sujada, za ta zama kamar abin ɗamaran nan, wanda ba shi da sauran amfani.

Karanta cikakken babi Irm 13