Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 8:3-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Nilu zai cika da kwaɗi, za su tashi, su shiga cikin fādarka, da ɗakin kwanciyarka, da gadonka, har da gidajen fadawanka da jama'arka. Za su kuma shiga matuyanka da kwanon tuwonka,

4. har ma za su hau bisa kanka, da jama'arka, da dukan fādawanka.’ ”

5. Sai Ubangiji ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya miƙa sandansa a bisa koguna, da rufuffuka, da tafkuna don ya sa kwaɗi su fito, su rufe ƙasar Masar.

6. Haruna ya miƙa sandansa a bisa ruwayen Masar, kwaɗi kuwa suka fito, suka rufe ƙasar Masar.

7. Masu sihiri kuma suka sa kwaɗi su fito a bisa ƙasar Masar ta wurin sihirinsu.

8. Sai Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna, ya ce su roƙi Ubangiji ya kawar masa da kwaɗin, shi da mutanensa, sa'an nan zai saki jama'ar, su tafi su miƙa wa Ubangiji hadaya.

9. Musa ya ce wa Fir'auna, “In ka yarda, a wane lokaci ne kake so in roƙa maka, kai da barorinka da jama'arka domin a kawar da kwaɗin daga gidajenku, a hallakar muku da su, sai dai na cikin Kogin Nilu za a bari?”

10. Fir'auna ya ce, “Gobe ne.”Musa kuwa ya ce, “Za a yi kamar yadda ka faɗa, domin ka sani babu wani allah kamar Ubangiji Allahnmu.

11. Kwaɗin za su rabu da ku, da kai, da gidanka, da fādawanka, da jama'arka, sai na cikin Nilu kaɗai za a bari.”

12. Da Musa da Haruna suka fita daga gaban Fir'auna, sai Musa ya roƙi Ubangiji ya kawar da kwaɗin nan da suka azabta wa Fir'auna.

13. Ubangiji kuwa ya karɓi addu'ar Musa, sai kwaɗin da suke cikin gida da waɗanda suke kewaye da gida, da waɗanda suke cikin saura suka mutu.

14. Aka tsiba su tsibi tsibi. Suka sa ƙasar ta yi ɗoyi.

15. Da Fir'auna ya ga an kawar masa da kwaɗin, sai ya taurare zuciyarsa, ya ƙi jinsu kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

16. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya miƙa hannunsa ya bugi ƙurar ƙasar, ta zama kwarkwata a ƙasar Masar.

17. Haka kuwa suka yi. Haruna ya miƙa sandansa ya bugi ƙurar ƙasa, sai ta zama kwarkwata a bisa 'yan adam, da bisa dabbobi. Dukan ƙurar ta zama kwarkwata ko'ina cikin ƙasar Masar.

18. Masu sihiri suka ƙokarta su sa kwarkwata ta bayyana ta wurin sihirinsu, amma ba su iya ba. Kwarkwata kuma ta yayyaɓe 'yan adam da dabbobi.

19. Sai masu sihiri suka ce wa Fir'auna, “Ai, wannan aikin Allah ne.” Amma zuciyar Fir'auna ta taurare, har da bai kasa kunne ga Musa da Haruna ba, kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

Karanta cikakken babi Fit 8