Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 8:10-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Fir'auna ya ce, “Gobe ne.”Musa kuwa ya ce, “Za a yi kamar yadda ka faɗa, domin ka sani babu wani allah kamar Ubangiji Allahnmu.

11. Kwaɗin za su rabu da ku, da kai, da gidanka, da fādawanka, da jama'arka, sai na cikin Nilu kaɗai za a bari.”

12. Da Musa da Haruna suka fita daga gaban Fir'auna, sai Musa ya roƙi Ubangiji ya kawar da kwaɗin nan da suka azabta wa Fir'auna.

13. Ubangiji kuwa ya karɓi addu'ar Musa, sai kwaɗin da suke cikin gida da waɗanda suke kewaye da gida, da waɗanda suke cikin saura suka mutu.

14. Aka tsiba su tsibi tsibi. Suka sa ƙasar ta yi ɗoyi.

15. Da Fir'auna ya ga an kawar masa da kwaɗin, sai ya taurare zuciyarsa, ya ƙi jinsu kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

16. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya miƙa hannunsa ya bugi ƙurar ƙasar, ta zama kwarkwata a ƙasar Masar.

17. Haka kuwa suka yi. Haruna ya miƙa sandansa ya bugi ƙurar ƙasa, sai ta zama kwarkwata a bisa 'yan adam, da bisa dabbobi. Dukan ƙurar ta zama kwarkwata ko'ina cikin ƙasar Masar.

18. Masu sihiri suka ƙokarta su sa kwarkwata ta bayyana ta wurin sihirinsu, amma ba su iya ba. Kwarkwata kuma ta yayyaɓe 'yan adam da dabbobi.

19. Sai masu sihiri suka ce wa Fir'auna, “Ai, wannan aikin Allah ne.” Amma zuciyar Fir'auna ta taurare, har da bai kasa kunne ga Musa da Haruna ba, kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

20. Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe ka sami Fir'auna a daidai lokacin da ya fita za shi rafi, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada.

21. In kuwa ka ƙi sakin jama'ata, sai in koro maka ƙudaje, da kai da fādawanka, da jama'arka, da gidajen Masarawa, har ma duk da ƙasa inda suke takawa.

Karanta cikakken babi Fit 8