Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 7:18-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Kifayen da suke cikin Nilu za su mutu. Nilu kuwa zai yi ɗoyi, har da Masarawa ba za su iya shan ruwansa ba.”’

19. Ubangiji kuma ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya ɗauki sandansa ya miƙa shi a bisa ruwayen Masar, da kogunansu, da rafuffukansu, da fadamunsu, da dukan tafkunansu don ruwansu ya zama jini. Jini zai kasance ko'ina a ƙasar Masar, i, har ma cikin randuna.

20. Musa da Haruna kuwa suka yi daidai kamar yadda Ubangiji ya umarta. Sai Haruna ya ta da sandansa sama ya bugi ruwan Nilu a gaban Fir'auna da fādawansa. Dukan ruwan Nilu kuwa ya rikiɗe jini.

21. Kifayen da suke cikin Nilu suka mutu. Nilu kuwa ya yi ɗoyi, har Masarawa ba su iya shan ruwansa ba. Ko'ina kuma a ƙasar Masar akwai jini.

22. Masu sihiri kuma na Masar suka yi haka, su ma, ta wurin sihirinsu, don haka zuciyar Fir'auna ta daɗa taurarewa, ya kuwa ƙi jin Musa da Haruna kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

23. Sai ya juya, ya koma fādarsa, bai ko kula da abin da aka yi ba.

24. Dukan Masarawa suka tattone ramummuka a bakin Nilu, suna neman ruwan sha, gama ba su iya shan ruwan Nilu ba.

25. Kwana bakwai suka cika bayan da Ubangiji ya bugi Kogin Nilu.

Karanta cikakken babi Fit 7