Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 5:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan wannan Musa da Haruna suka tafi gaban Fir'auna, suka ce, “Ga abin da Ubangjiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Bar jama'ata su tafi domin su yi mini idi cikin jeji.”’

2. Amma Fir'auna ya ce, “Wane ne Ubangiji, har da zan ji maganarsa, in bar Isra'ilawa su tafi? Ai, ban san Ubangiji ɗin nan ba, balle in bar Isra'ilawa su tafi.”

3. Sai suka ce, “Allahn Ibraniyawa ya gamu da mu, muna roƙonka, ka bar mu mu yi tafiyar kwana uku cikin jeji domin mu yi wa Ubangiji Allahnmu hadaya, don kada ya aukar mana da annoba ko takobi.”

4. Amma Sarkin Masar ya ce wa Musa da Haruna, “Me ya sa kuke hana jama'ar yin aikinsu? Ku tafi wurin aikin gandunku.”

5. Ya kuwa ci gaba ya ce, “Ga jama'ar ƙasar sun yi yawa, yanzu kuna so ku hana su yin aikinsu.”

6. A ran nan fa Fir'auna ya umarci shugbannin aikin gandu da manyan jama'a, ya ce,

7. “Nan gaba kada ku ƙara ba mutanen nan budu na yin tubali kamar dā. Ku sa su, su tafi, su tara budu da kansu.

8. Duk da haka, kada su kāsa cika yawan tubalin da aka ƙayyade musu da fari. Ai, su ragwaye ne, shi ya sa suke kuka, suna cewa, ‘A bar mu, mu tafi mu miƙa wa Allahnmu hadaya.’

9. Ku sa mutanen su yi aiki mai tsanani har da ba za su sami damar kasa kunne ga maganganun ƙarya ba.”

10. Sai shugabannin aikin gandu da manyan jama'a suka tafi suka faɗa wa jama'a cewa, “Ga abin da Fir'auna ya ce, ‘Ba zan ba ku budu ba.

11. Ku je, ku da kanku, ku nemi budu inda duk za ku iya samowa, amma daɗai, ba za a sawwaƙe muku aikinku ba.”’

Karanta cikakken babi Fit 5