Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 40:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa,

2. “A kan rana ta fari ga wata na fari za ka kafa alfarwa ta sujada.

3. Sai ka sa akwatin alkawari a cikinta sa'an nan ka kāre shi da labule.

4. Ka shigar da tebur ɗin, ka shirya kayayyakinsa daidai. Ka kuma shigar da alkukin, ka sa fitilu a bisansa.

5. Ka ajiye bagade na zinariya na ƙona turare a gaban akwatin alkawari, sa'an nan ka rataya labulen ƙofar alfarwa.

6. Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar alfarwa ta sujada,

7. ka kuma ajiye daro tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, sa'an nan ka zuba ruwa a ciki.

8. Sai ka yi farfajiya ka kewaye wurin sa'an nan ka rataya labulen ƙofar farfajiyar.

9. “Ka ɗauki man keɓewa, ka shafa wa alfarwa da dukan abin da yake cikinta, domin ka tsarkake ta da kayayyakinta duka, za ta kuwa zama tsarkakakkiya.

10. Ka shafa wa bagade na ƙona hadaya da kayayyakinsa duka man domin ka tsarkake shi, bagaden kuma zai zama mafi tsarki.

11. Ka kuma shafa wa daron da gammonsa man keɓewa, da haka za ka tsarkake shi.

12. “Ka kuma kawo Haruna da 'ya'yansa maza a ƙofar alfarwa ta sujada, ka yi musu wanka da ruwa.

13. Sa'an nan ka sa wa Haruna tufafi tsarkaka ka shafa masa man domin ka tsarkake shi ya yi mini aiki na firist.

Karanta cikakken babi Fit 40