Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Kafawar Alfarwa ta Sujada da Keɓewarta

1. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa,

2. “A kan rana ta fari ga wata na fari za ka kafa alfarwa ta sujada.

3. Sai ka sa akwatin alkawari a cikinta sa'an nan ka kāre shi da labule.

4. Ka shigar da tebur ɗin, ka shirya kayayyakinsa daidai. Ka kuma shigar da alkukin, ka sa fitilu a bisansa.

5. Ka ajiye bagade na zinariya na ƙona turare a gaban akwatin alkawari, sa'an nan ka rataya labulen ƙofar alfarwa.

6. Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar alfarwa ta sujada,

7. ka kuma ajiye daro tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, sa'an nan ka zuba ruwa a ciki.

8. Sai ka yi farfajiya ka kewaye wurin sa'an nan ka rataya labulen ƙofar farfajiyar.

9. “Ka ɗauki man keɓewa, ka shafa wa alfarwa da dukan abin da yake cikinta, domin ka tsarkake ta da kayayyakinta duka, za ta kuwa zama tsarkakakkiya.

10. Ka shafa wa bagade na ƙona hadaya da kayayyakinsa duka man domin ka tsarkake shi, bagaden kuma zai zama mafi tsarki.

11. Ka kuma shafa wa daron da gammonsa man keɓewa, da haka za ka tsarkake shi.

12. “Ka kuma kawo Haruna da 'ya'yansa maza a ƙofar alfarwa ta sujada, ka yi musu wanka da ruwa.

13. Sa'an nan ka sa wa Haruna tufafi tsarkaka ka shafa masa man domin ka tsarkake shi ya yi mini aiki na firist.

14. Sai ka kawo 'ya'yan Haruna maza, ka kuma sa musu taguwoyi.

15. Sa'an nan ka shafa musu mai kamar yadda ka shafa wa mahaifinsu domin su yi mini aiki a matsayin firistoci. Shafa musu man zai sa su zama firistoci din din din dukan zamanansu.”

16. Haka kuwa Musa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.

17. A rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu, aka kafa alfarwa.

18. Sai musa ya kafa alfarwa, ya kafa kwasfanta, ya jera katakanta, ya sa mata sandunanta, ya kakkafa dirkokinta.

19. Sa'an nan ya shimfiɗa murfi a bisa alfarwa ya rufe alfarwar kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

20. Sai ya ɗauki dokoki goma ɗin, ya sa a akwatin, ya kuma zura sandunan a ƙawanen akwatin, sa'an nan ya sa murfin a bisansa.

21. Ya kawo akwatin a cikin alfarwa, sa'an nan ya sa labulen don kāre akwatin alkawari, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

22. Musa ya sa teburin cikin alfarwa ta sujada, a wajen gefen arewa na alfarwa, a gaban labulen.

23. Sa'an nan ya jera gurasa daki-daki a bisa teburin a gaban Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

24. Ya kuma sa alkukin a cikin alfarwa ta sujada daura da teburin a wajen gefen kudu na alfarwa.

25. Ya kunna fitilun a gaban Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

26. Ya kuma sa bagade na zinariya a cikin alfarwa ta sujada daga gaban labulen.

27. Sai ya ƙona turare mai ƙanshi a bisansa kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

28. Ya sa labule a ƙofar alfarwa.

29. Ya kuma sa bagade na ƙona hadaya a ƙofar alfarwa ta sujada, sa'an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da ta gari kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

30. Ya kuma sa daro a tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, sa'an nan ya zuba ruwa a ciki don wanka.

31. A cikinsa Musa da Haruna da 'ya'yansa maza sukan wanke hannuwansu da ƙafafunsu,

32. sa'ad da suke shiga cikin alfarwa ta sujada, da sa'ad da sukan kusaci bagaden kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

33. Ya kuma yi farfajiya kewaye da alfarwa da bagaden, ya sa labulen ƙofar farfajiyar. Da haka Musa ya gama aikin.

Saukowar Girgije a bisa Alfarwa ta Sujada

34. Sa'an nan girgije ya rufe alfarwa ta sujada, ɗaukakar Ubangiji kuma ta cika alfarwa.

35. Musa kuwa bai iya shiga alfarwa ta sujada ba domin girgijen yana zaune a bisanta, ɗaukakar Ubangiji kuma ta cika alfarwa.

36. Cikin tafiyar Isra'ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa'ad da girgijen ya tashi daga kan alfarwa.

37. Idan girgijen bai tashi ba, su kuma ba za su tashi ba, sai a ranar da ya tashi.

38. Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan alfarwa da rana, da dare kuwa wuta yake cikinsa domin dukan Isra'ilawa su gani.