Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 4:12-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Yanzu fa, tafi, zan kasance tare da bakinka, in koya maka abin da za ka faɗa.”

13. Amma Musa ya ce, “Ya Ubangijina, in ka yarda, ka aiki wani.”

14. Ubangiji kuwa ya hasala da Musa, ya ce, “Haruna ɗan'uwanka Balawe ba ya nan ne? Lalle na san shi ya iya magana, ga shi nan ma, yana fitowa ya tarye ka. Sa'ad da ya gan ka kuwa zai yi murna cikin zuciyarsa.

15. Sai ka yi magana da shi. Ka kuma sa masa maganata a baka, zan kuwa kasance tare da bakinka da bakinsa. Zan kuma sanar da ku abin da za ku yi.

16. Shi zai yi maka magana da jama'a, zai zama bakinka, kai kuwa za ka zama kamar Allah a gare shi.

17. Za ka riƙe wannan sanda a hannunka, da shi za ka aikata mu'ujizan.”

18. Musa ya koma wurin Yetro, surukinsa, ya ce masa, “Ina roƙonka, ka bar ni in koma wurin 'yan'uwana a Masar, in ga ko a raye suke har yanzu.”Sai Yetro ya ce wa Musa, “Ka tafi lafiya.”

19. Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa a Madayana, ya koma Masar, gama dukan waɗanda suke neman ransa sun rasu.

20. Saboda haka Musa ya ɗauki matarsa da 'ya'yansa maza, ya haushe su bisa kan jaki, ya koma ƙasar Masar, yana riƙe da sandan Allah a hannunsa.

21. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Sa'ad da ka koma Masar, sai ka kula, ka aikata a gaban Fir'auna dukan mu'ujizan da na sa cikin ikonka. Amma zan taurara zuciyarsa, don kada ya bar jama'a su fita.

22. Za ka ce wa Fir'auna, Ubangiji ya ce, ‘Isra'ila ɗan fārina ne.

23. Na ce maka ka bar ɗana ya tafi domin ya bauta mini, amma in ka ƙi ka bar shi ya tafi, yanzu zan kashe ɗan fārinka.”’

24. Ya zama kuwa sa'ad da Musa yake masauki a kan hanya sai Ubangiji ya gamu da shi, ya nema ya kashe shi.

25. Sai Ziffora ta ɗauki ƙanƙara ta yanke loɓar ɗanta, ta taɓa gaban Musa da shi, ta ce, “Kai angon jini kake a gare ni.”

26. Sa'an nan Ubangiji ya ƙyale shi. Ta kuma ce, “Kai angon jini ne,” saboda kaciyar.

Karanta cikakken babi Fit 4