Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 35:27-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Su shugabanni suka kawo duwatsu masu daraja da za a jera a kan falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

28. Suka kuma kawo kayan yaji, da man fitila, da man keɓewa, da turaren ƙonawa.

29. Sai dukan mata da maza na Isra'ilawa waɗanda zuciyarsu ta iza su, suka kawo kowane irin abu domin yin aikin da Ubangiji ya umarci Musa. Suka kawo sadaka ta yardar rai ga Ubangiji.

30. Sai Musa ya ce wa Isra'ilawa, “Ga shi, Ubangiji ya zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza.

31. Ya cika shi da ruhu na hikima, da basira, da sani, da fasaha na iya yin kowane irin aiki.

32. Domin ƙirƙiro zāne-zāne na gwaninta, waɗanda za a yi da zinariya, da azurfa, da tagulla.

33. Haka kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa, da sassaƙar itace, da kowane irin aiki na gwaninta.

34. Ubangiji ya ba Bezalel, da Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, hikimar koya wa waɗansu sana'a.

35. Gama ya cika su da hikima ta yin kowane irin aiki na sassaƙa da na zāne-zāne, da na yin ɗinke-ɗinke da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin, da na yin saƙa. Sun iya yin kowane irin aiki da yin zāne-zāne.

Karanta cikakken babi Fit 35