Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 34:3-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Kada wani mutum ya zo tare da kai, kada a ga kowane mutum a ko'ina a kan dutsen, kada a bar garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu su yi kiwo kusa da dutsen.”

4. Sai Musa ya sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ya tashi da sassafe, ya hau Dutsen Sina'i, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya riƙe allunan nan biyu na dutse a hannunsa.

5. Ubangiji kuwa ya sauko cikin girgije ya tsaya tare da shi a can, ya yi shelar sunansa.

6. Ya kuma gifta a gaban Musa, ya ce, “Ni ne Ubangiji, Ubangiji Allah mai jinƙai, mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna, mai gaskiya.

7. Ni ne mai nuna ƙauna ga dubbai, mai gafarta mugunta, da laifi, da zunubi, wanda ba zai kuɓutar da mai mugunta ba, amma saboda laifin iyaye nakan hukunta 'ya'ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu.”

8. Sai Musa ya hanzarta, ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya yi sujada.

9. Ya ce, “Idan na sami tagomashi a gare ka, ya Ubangiji, ina roƙonka, ka yi tafiya tare da mu, ko da yake jama'a masu taurinkai ne, ka gafarta laifinmu, da zunubinmu, ka sa mu zama abin gādonka.”

10. Allah kuwa ya ce, “Ga shi, na yi alkawari, cewa a gaban dukan jama'a zan aikata al'ajabai irin waɗanda ba a taɓa aikatawa a duniya ba, ko cikin wata al'umma. Dukan mutanen da kuke zaune tare da su za su ga aikina, gama zan aikata abin bantsoro a cikinku.

Karanta cikakken babi Fit 34