Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 34:1-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce wa Musa, “Sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farkon, ni kuwa in rubuta kalmomin da suke cikin alluna na farko da ka farfasa.

2. Da safe ka shirya, ka zo Dutsen Sina'i ka gabatar da kanka gare ni a kan dutsen.

3. Kada wani mutum ya zo tare da kai, kada a ga kowane mutum a ko'ina a kan dutsen, kada a bar garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu su yi kiwo kusa da dutsen.”

4. Sai Musa ya sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ya tashi da sassafe, ya hau Dutsen Sina'i, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya riƙe allunan nan biyu na dutse a hannunsa.

5. Ubangiji kuwa ya sauko cikin girgije ya tsaya tare da shi a can, ya yi shelar sunansa.

6. Ya kuma gifta a gaban Musa, ya ce, “Ni ne Ubangiji, Ubangiji Allah mai jinƙai, mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna, mai gaskiya.

7. Ni ne mai nuna ƙauna ga dubbai, mai gafarta mugunta, da laifi, da zunubi, wanda ba zai kuɓutar da mai mugunta ba, amma saboda laifin iyaye nakan hukunta 'ya'ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu.”

8. Sai Musa ya hanzarta, ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya yi sujada.

9. Ya ce, “Idan na sami tagomashi a gare ka, ya Ubangiji, ina roƙonka, ka yi tafiya tare da mu, ko da yake jama'a masu taurinkai ne, ka gafarta laifinmu, da zunubinmu, ka sa mu zama abin gādonka.”

10. Allah kuwa ya ce, “Ga shi, na yi alkawari, cewa a gaban dukan jama'a zan aikata al'ajabai irin waɗanda ba a taɓa aikatawa a duniya ba, ko cikin wata al'umma. Dukan mutanen da kuke zaune tare da su za su ga aikina, gama zan aikata abin bantsoro a cikinku.

11. Ku kiyaye abin da na umarce ku a wannan rana. Ga shi, zan kora muku Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

12. Ku fa kula da kanku, kada ku kuskura, ku ƙulla alkawari da mazaunan ƙasar inda za ku tafi, don kada su zama muku alƙalai.

13. Sai ku rurrushe bagadansu, ku farfashe al'amudansu, ku sassare gumakansu.

14. “Ba za ku yi wa wani allah sujada ba, sai dai ni, gama sunana Mai Kishi, gama ni Allah mai kishi ne.

15. Kada ku ƙulla alkawari da mazaunan ƙasar don kada sa'ad da suke shagulgulan bidi'arsu ga allolinsu, suna miƙa musu hadaya, waninsu ya gayyace ku ku ci abin hadayarsa.

16. Kada kuma ku auro wa 'ya'yanku maza 'yan matansu 'ya'ya matansu kuma su yi shagulgulan bidi'ar allolinsu, har su sa 'ya'yanku su bi allolinsu.

Karanta cikakken babi Fit 34