Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 29:7-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Ka kuma ɗauki man keɓewa, ka zuba masa a ka domin ka keɓe shi.

8. “Sa'an nan ka kawo 'ya'yansa maza, ka sa musu zilaikun.

9. Ka kuma ɗaura musu ɗamara, ka sa musu hulunan. Aikin firist kuwa zai zama nasu har abada bisa ga dokar. Haka za ka keɓe Haruna da 'ya'yansa maza.

10. “A kuma kawo bijimin a ƙofar alfarwa ta sujada. Haruna da 'ya'yansa maza za su ɗora hannuwansu a kan bijimin.

11. Za ka yanka bijimin a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada.

12. Za ka ɗibi jinin bijimin ka sa a bisa zankayen bagaden da yatsanka. Sauran jinin kuwa ka zuba a gindin bagaden.

13. Ka cire dukan kitsen da yake rufe da kayan cikin, da kitsen da yake manne da hanta, da wanda yake manne a ƙoda biyu ɗin. Ka ƙone su a bisa bagaden.

14. Amma naman bijimin da fatarsa, da tarosonsa, za ka ƙone da wuta a bayan zango, wannan hadaya ce don zunubi.

15. “Sai a kawo rago ɗaya, Haruna kuwa da 'ya'yansa maza su ɗora hannuwansu a bisa ragon.

16. Sa'an nan ka yanka ragon, ka ɗibi jininsa, ka yayyafa shi kewaye a kan bagaden.

17. Ka kuma yanyanka rago gunduwa-gunduwa, ka wanke kayan cikinsa, da ƙafafunsa, ka haɗa su da gunduwoyin, da kan.

18. Sa'an nan ka ƙone ragon duka a bisa bagaden don ya ba da ƙanshi. Wannan hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, wato hadayar da aka ƙone da wuta.

Karanta cikakken babi Fit 29