Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 29:23-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Daga cikin kwandon abinci marar yistin da yake a gaban Ubangiji, sai ka ɗauki malmala ɗaya, da waina ɗaya da aka yi da mai, da ƙosai ɗaya.

24. Za ka sa waɗannan duka a hannun Haruna da na 'ya'yansa maza. Sai su kaɗa su domin hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji.

25. Sa'an nan za ka karɓe su daga hannunsu, ka ƙone su a bisa bagaden kamar hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Ita hadaya ce ta ƙonawa da wuta ga Ubangiji.

26. “Za ka ɗauki ƙirjin ragon da aka yanka don keɓewar Haruna, ka kaɗa shi don hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. Wannan ƙirji zai zama rabonka.

27. Za ka tsarkake ƙirji na hadaya ta kaɗawa, da cinya ta hadaya ta ɗagawa da za a kaɗa a kuma ɗaga na ragon keɓewa, wanda yake na Haruna da wanda yake na 'ya'yansa maza.

28. Wannan zai zama rabon Haruna da na 'ya'yansa maza daga wurin Isra'ilawa. Gama wannan hadaya ta ɗagawa ce daga cikin hadayu na salama da Isra'ilawa za su miƙa wa Ubangiji.

29. “Keɓaɓɓun tufafin nan na Haruna za su zama na 'ya'yansa maza bayan rasuwarsa. Da tufafin nan ne za a zuba musu mai, a keɓe su.

30. Ɗan da ya gāje shi a matsayin firist shi ne zai sa su har kwana bakwai, lokacin da ya shiga alfarwa ta sujada, domin ya yi aiki a Wuri Mai Tsarki.

31. “Sai ka ɗauki naman ragon keɓewa, ka dafa shi a wuri mai tsarki.

32. Haruna da 'ya'yansa maza za su ci naman da abinci da yake a cikin kwandon a ƙofar alfarwa ta sujada.

33. Za su ci abubuwan nan da aka yi kafara da su a lokacin tsarkakewarsu da keɓewarsu. Ba wanda zai ci, sai su kaɗai, gama abubuwan nan tsarkaka ne.

34. Amma idan naman keɓewar ko abincin ya ragu har safiya, sai ka ƙone abin da ya ragu, kada a ci, gama tsattsarka ne.

Karanta cikakken babi Fit 29