Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 29:16-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Sa'an nan ka yanka ragon, ka ɗibi jininsa, ka yayyafa shi kewaye a kan bagaden.

17. Ka kuma yanyanka rago gunduwa-gunduwa, ka wanke kayan cikinsa, da ƙafafunsa, ka haɗa su da gunduwoyin, da kan.

18. Sa'an nan ka ƙone ragon duka a bisa bagaden don ya ba da ƙanshi. Wannan hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, wato hadayar da aka ƙone da wuta.

19. “A kuma kawo ɗayan ragon, Haruna kuma da 'ya'yansa maza su ɗora hannuwansu a bisa ragon.

20. Sa'an nan ka yanka ragon, ka ɗibi jininsa ka shafa bisa leɓatun kunnen Haruna na dama, da bisa leɓatun kunnuwan 'ya'yansa maza na dama, da a kan manyan yatsotsin hannuwansu na dama, da kuma a kan manyan yatsotsin ƙafafunsu na dama. Sauran jinin kuwa, sai ka yayyafa shi a kewaye a kan bagaden.

21. Ka ɗiba daga cikin jinin da yake bisa bagaden, da man keɓewa, ka yayyafa wa Haruna da tufafinsa, da bisa 'ya'yansa maza, da tufafinsu don a tsarkake Haruna, da 'ya'yansa maza, da tufafinsu.

Karanta cikakken babi Fit 29